Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Nijeriya ya kai 190
2020-04-04 15:30:42        cri

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana a jiya cewa, yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar dake yammacin Afrika ya kai 190.

Sabon rahoton cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, ya nuna cewa, an samu sabbin mutane 6 da suka kamu da cutar a jihar Osun dake kudu maso yammacin kasar.

Lamarin da ya kawo adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar zuwa 190, inda Lagos, wato cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar ke da mutane 98, sai birnin Abuja dake bi mata baya da mutane 38 da suka harbu.

Cibiyar NCDC ta ce jimilar mutane 20 ne suka warke, aka kuma sallama daga asibiti, inda suka koma harkokinsu na yau da kullum. Ta kuma bayyana cewa mutane 2 sun mutu a Abuja, kuma dukkansu na dauke da wasu cututtuka na daban baya ga COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China