Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sanarwar yanke hulda tsakanin Amurka da WHO ta haifar da ce-ce ku-ce da suka a kasa da kasa
2020-05-31 20:46:08        cri

A ranar Juma'a shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa, kasarsa ta yanke duk wata hulda dake tsakaninta da hukumar WHO, kana ta ayyana sauya akalar kudaden da take tallafawa hukumar zuwa wani bangaren na daban.

Sanarwar ta haifar da ce-ce ku-ce da kuma suka a kasa da kasa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Mousavi ya wallafa a shafin sada zumunta a ranar 30 ga watan Mayu, inda ya ce, a daidai lokacin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duk duniya, kasar Amurka ta katse huldar dake tsakaninta da hukumar WHO, wanda ya bude sabon babi kan jerin janyewar da kasar ta tsara yi.

Mousavi ya kara da cewa, gwamnatin Amurka tana neman hanyar fakewa ne domin boye gazawar da ta yi na kasa cika alkawarin da ta daukawa mutane. Amma wannan neman yin watsi da hakkin dake bisa wuyanta ba zai iya rudar duniya ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova ta fada a ranar Juma'a cewa, Amurka ta kawo koma baya ga tanadin dokar hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya a daidai lokacin da duniya take tsananin bukatar yin hadin gwiwa don yaki da annobar. Gazawar fannin kiwon lafiyar Amurka a wannan lokacin da ake fama da barkewar annoba ya kara nunawa a fili rashin cancantar Amurka wajen tsoma baki kan shugabantar fannin kiwon lafiya.

Babban jami'in kungiyar tarayyar Turai EU da babban jami'in diflomasiyya sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, kungiyar za ta ci gaba da tallafawa hukumar lafiyar ta duniya, sannan sun bukaci gwamnatin Amurka ta sake tunani kan kudirinta na yanke alaka da hukumar ta WHO.

Ursula von der Leyen, shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Turai, da Josep Borrell, babban wakilin EU kan al'amurran kasa da kasa da manufofin tsaro, sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, ya kamata hukumar WHO ta ci gaba da ba da jagoranci wajen aikin dakile annoba a matakin kasa da kasa, a halin yanzu da kuma a nan gaba. Game da wannan, ana matukar bukatar goyon baya da kuma tallafi daga kowane bangare. A yayin da duniya ke fama da kalubaloli, yanzu lokaci ne da ya dace a hada gwiwa domin neman mafita tare. Dole ne a kaucewa duk wasu abubuwa da za su kawowa kasa da kasa mummunan sakamako.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China