Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Los Angeles na Amurka ya sanar da hana fita da dare domin dakile tashin hankali
2020-05-31 17:18:20        cri

A jiya Asabar 30 ga wata, magajin garin birnin Los Angeles, Eric Garcetti, ya sanar da kafa dokar hana fita da dare a birnin saboda tashe-tashen hankula da dama da suka faru a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kana ya bukaci gwamnan jihar California da ya tura jami'an tsaro ga birnin domin kwantar da kura.

A cikin kwanaki hudu da suka gabata, an yi zanga-zanga da dama a birnin Los Angeles domin nuna adawa ga 'yan sanda farar fata na birnin Minneapolis na jihar Minnesota ta kasar sakamakon kisan gillar da suka yiwa George Floyd, 'dan asalin Afirka har ya mutu, ya zuwa daren ranar 29 ga wata, 'yan sanda da masu zanga-zanga suna cikin fargaba, daga baya 'yan sanda sun kama masu zanga-zanga da yawansu ya kai 533, a yammacin jiya, an ci gaba da yin zanga-zanga a birnin Los Angeles, inda zanga-zangar da aka yi a yankin Fairfax ta fi tsanani, masu zanga-zanga da yawansu ya kai sama da dubu daya sun tafi kan tituna, har sun lalata wasu motocin 'yan sanda, tare kuma da lalata wasu kantuna.

Magajin garin Los Angeles, Eric Garcetti, ya bayyana cewa, birnin yana gamuwa da masifu guda biyu wato barkewar annobar COVID-19 da tashin hankali, kuma an rufe daukacin wuraren binciken kwayar cutar a birnin bisa dalilin aukuwar tashin hankali, don haka jami'an kiwon lafiya suna nuna damuwa matuka, saboda idan an gano wanda ya kamu da cutar a cikin masu zanga-zanga, lamarin zai sa kokarin dakile annobar da ake a birnin ya watse.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China