Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu wani dan Nijeriya dake Sin da ya kamu da cutar coronavirus
2020-02-16 16:55:11        cri

Bisa labarin da jaridar The Guardian ta kasar Nijeriya ta bayar a ranar 14 ga wata, an ce, wani dalibin kasar Nijeriya dake karatu a jami'ar Lanzhou ta kasar Sin ya bayyana wa jaridar cewa, yawan dalibai 'yan Nijeriya dake birnin Lanzhou na lardin Gansu ya kai kimanin 150, ya zuwa yanzu babu mutum daya daga cikinsu da ya kamu da cutar. Ya ce a cikin makarantunsu, ana bukatar yin bincike kan zafin jikinsu, da sanya abin rufe baki da hanci, da wanke hannu ko da yaushe. Ko da yake ba a amince su fita daga makarantunsu ba, amma ana tabbatar da kulawa da rayuwarsu yadda ya kamata.

An ruwaito ministan kiwon lafiya na Nijeriya yana cewa, a halin yanzu, ana bukatar 'yan Nijeriyar dake kasar Sin su zauna a cikin gidajensu, an samar da kayayyakin bukatun yau da kullum yadda ya kamata, ciki har da kayayyakin magance cutar. Ministan ya yi kira ga jama'ar kasar Nijeriya da su kaucewa duk wata jita-jitar da ake yadawa ta shafukan internet, ya zuwa yanzu babu wani dan kasar Nijeriya da ya kamu da cutar coronavirus, suna rayuwa a kasar Sin cikin goshin lafiya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China