Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tura jiragen kasa na zamani zuwa Nijeriya
2020-02-18 20:15:08        cri

A yau ne, aka fara yin jigilar jiragen kasa na zamani guda biyu da kamfanin kera jiragen kasa da motoci na Dalian na kasar Sin ya kera ta jiragen ruwa, inda za a yi amfani da su a birnin Abuja, babban birnin kasar Nijeriya.

Wannan shi ne karon farko da kamfanin Dalian ya kera wadannan jiragen kasa guda biyu, wadanda ke gudun kilomita 100 a cikin kowace sa'a.

An kera jiragen kasa ne da yadda za su dace da yanayin birnin Abuja na kasar Nijeriya, wato zafi, da ruwan sama da iska tare da kuma yawan rairayi, don haka injunan jiragen suna iya jure iska mai karfi, da rairayi, da yanayin zafi, da ruwan sama, da motsi mai tsanani da sauransu, za kuma su iya yin tafiya cikin tsaro.

Kamfanin Dalian ya bayyana cewa, wadannan jiragen kasa da ya kera wa kasar Nijeriya za su ba da gudummawa ga fannin raya kasuwar zirga-zirgar jiragen kasa ta nahiyar Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China