Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Ya Kamata Mu Nemi Damammakin Ci Gaba Cikin Kalubaloli
2020-05-23 23:21:16        cri
Yau Asabar, yayin da yake halartar cikakken zaman taron 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa mai kula da tattalin arziki ta kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, wasu kasashen duniya sun nuna ra'ayin kariyar ciniki, amma, kasar Sin tana tsayawa tsayin dake kan kare tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa da kuma raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa ra'ayin dimokuradiyya. A nan gaba kuma, za ta ci gaba da neman bunkasuwa bisa ka'idojin bude kofa ga waje, da hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, domin inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta fuska mai bude kofa ga waje da fahimtar juna da cimma daidaito da kuma cimma moriyar juna, ta yadda za a gina tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga waje.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauyen bunkasuwar tattalin arziki, da kyautatuwar tsarin tattalin arziki, lamarin da ya kawo sabbin damammakin raya tattalin arzikin, da kuma wasu matsaloli ta fuskar wannan tsari. A sa'i daya kuma, bullar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta matsa wa harkokin tattalin arzikin kasar Sin lamba sosai.

Bugu da kari, Xi ya ce, kasar Sin tana kuma fuskantar wasu kalubalolin kasuwannin kasa da kasa, shi ya sa, ya kamata kasar Sin ta ci gaba da neman bunkasuwa cikin yanayin rashin tabbas.

Amma, ya ce, kasar Sin tana da cikakken tsarin masana'antu, da babban karfin samar da kayayyaki, da masanan kimiyya da fasaha da kwararru sama da miliyan 170, har ma tana da babbar kasuwa mai kunshe da mutane biliyan 1.4, haka kuma, kasar Sin tana cikin muhimmin lokacin raya masana'antu na zamani da aikin sadarwa na zamani da birane na zamani da kuma aikin gona na zamani, shi ya sa, ake bukatar zuba jari a kasuwannin kasar Sin kwarai da gaske.

A nan gaba kuma, ya ce, ya kamata a gudanar da ayyuka bisa bukatun al'ummomin kasa, da gaggauta gina tsarin biyan bukatun al'ummar kasa, yayin inganta ayyukan kirkire-kirkire, domin samar da karin damammakin samun bunkasuwa.

A karshe dai, ya ce, a bana, ana da burin fitar da garuruwa 52 da kauyuka 2707 daga kangin talauci, da kuma karfafa aikin samar da ayyukan yi bisa dukkan fannoni. Haka kuma, ya kamata a inganta aikin ba da hidima ga masu fama da talauci, da ba da taimako ga kanannan kamfanoni don warware matsalolin da ake gamuwa da su. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China