Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Neman kyautata tattalin arziki bisa wani sabon yanayin da muke ciki
2020-05-23 22:15:42        cri

Ana ci gaba da gudanar da taron shekara-shekara na majalissar ba da shawara han harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, a yau Asabar, ya halarci taron wasu 'yan majalissar CPPCC masu kula da ayyukan tattalin arziki. Inda shugaban ya furta cewa, ya kamata a yi kokarin dogaro kan bukatun da ake samu a kasuwannin cikin gida, da kirkiro karin sabbin fasahohi, da raya wasu sabbin san'o'i masu alaka da fasahar injuna masu kwakwalwa, don samun karin fannoni masu taimakawa karuwar tattalin arziki, tare da gabatar da wasu bangarori masu karfi, wadanda kasar Sin za ta yi amfani da su don gudanar da hadin gwiwa da sauran kasashe.

Shugaban ya kara da cewa, ko da yake tattalin arzikin Sin na fuskantar matsin lamba, sakamakon wani yanayi na rashin tabbas da kwanciyar hankali da ake samu a duniya, kasar na da cikakken karfin tattalin arziki da jajircewa, kana tana da dabaru daban daban masu amfani da za ta iya dauka don tinkarar matsaloli. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China