Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya ce dole a sanya moriyar jama'a a gaban komai
2020-05-23 23:19:40        cri

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), Xi Jinping, ya halarci taron wakilan jama'ar jihar Mongoliya ta gida a jiya Juma'a, wanda ya gudana karkashin laimar taro karo na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13, inda ya jaddada muhimmancin alakar JKS da jama'ar kasar Sin. Ya ce dalilin da ya sa jam'iyyar ta yi kokarin daukar matakan raya kasa da gyare-gyare a kasar, shi ne neman sanya jama'a jin dadin zaman rayuwarsu.

Shugaban ya sa lura kan aikin kau da talauci a jihar Mongoliya ta gida, inda ya tambayi wani wakilin jama'a yadda ake gudanar da aikin a wurinsu. Haka zalika, ya tambayi wani wakilin jama'a na daban kan yadda ake kokarin kare muhallin hallitu a kan filayen ciyayi dake jihar.

Sa'an nan shugaban ya kara da cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ba ta da moriyar kanta, kana a ko da yaushe tana sanya moriyar jama'a a gaban kome. Ya ce, idan wata jam'iyya na son mulki mai dorewa, to dole ne ta yaukaka huldarta da jama'a, ta yi kokarin haye wahalhalu tare da su, gami da kokarin biyan bukatunsu.

A cewar shugaban, ya kamata a mai da aikin samar da alfanu ga jama'a ya zama mafi muhimmanci, saboda duk wani kokarin da ake yi na ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma gaba, ana yi ne domin neman biyan bukatun jama'a na samun zaman rayuwa mai inganci. Ya ce ya kamata a yi kokarin sanya jama'a ganin ci gaban harkoki, gami da amfanin su ta wasu hakikanan hanyoyi. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China