Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Wajibi ne a sanya kasuwa ta taka rawa mafi muhimmanci kan aikin raba albarkatu
2020-05-23 22:25:34        cri
A wajen taron wasu 'yan majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin masu kula da tattalin arizki da ya gudana a yau Asabar, a birnin Beijing na kasar Sin, wasu daga cikin 'yan majalissar sun ambaci bukatar kyautata tsarin raba albarkatu bisa bukatun da ake samu a kasuwanni.

Dangane da batun, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya nanata wajibcin sanya kasuwa ta taka rawa mafi muhimmanci kan aikin raba albarkatu tsakanin sassan al'ummu daban daban, kana dole ne a sanya gwamnati ita ma ta taka rawar gani a wannan fanni. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China