Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka rasu yayin harin bam a Somalia ya karu zuwa mutane 17
2019-07-23 10:48:10        cri

Rahotanni daga kasar Somalia na cewa, ya zuwa yammacin ranar Litinin, harin bam da aka kaddamar a wani shingen duba ababen hawa na jami'an tsaron kasar ya hallaka mutane 17, yayin da wasu mutanen 28 suka jikkata, ciki hadda mutane 12 dake cikin matsanancin yanayi.

Daraktan asibitin Medina dake birnin Mogadishu Mohamed Yusuf, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sun karbi gawawwakin mutane 17, baya ga wasu 28 da ke dauke da raunuka daban daban.

Rundunar 'yan sandan birnin ta ce fashewar ta auku ne da safiyar jiya Litinin, yayin da jami'an tsaro ke tsaka da binciken ababen hawa, a kan hanyar da ta nufi filin jiragen saman kasa da kasa na Aden Adde dake Mogadishu. Ga alama kuma, masu kaddamar da harin sun so hallaka jami'an tsaron dake wurin ne.

Kungiyar Al-Shabab wadda ta sha kaddamar da makamantan wadannan hare-hare kan jami'an gwamnatin kasar mai samun goyon bayan kasashen yamma, ta dauki alhakin harin na jiya Litinin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China