Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe da dama sun gabatar da daftarin yaki da cutar COVID-19 ga babban taron kiwon lafiyar duniya
2020-05-19 20:12:58        cri
Yau Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta halarci aikin tattaunawa, game da gabatar da daftarin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ga babban taron kiwon lafiyar duniya, tana kuma fatan za a zartas da daftarin, yayin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 73, da kuma aiwatar da daftarin yadda ya kamata.

Rahotanni na cewa, kungiyar tarayyar kasashen Turai, da kasar Rasha, da kasar Japan, da kasar Indiya, da kasar Brazil da kuma kasar Australia, da ma sauran kasashen da suka kai 120, sun gabatar da daftarin yaki da cutar COVID-19 ga babban taron kiwon lafiyar duniya.

Bugu da kari, Zhao Lijian ya ce, cikin daftarin, an nuna amincewa ga hukumar WHO, da ta jagoranci ayyuka masu nasaba da hakan, da kuma yin kira ga mambobin, da su hada kansu a fannonin nazarin kayayyakin bincike, da fasahohin jinya, da magani, da allurar rigakafi, da neman asalin cutar da dai sauransu, yayin da ake gudanar da bincike kan ayyukan da hukumar WHO ta yi ta fuskar yaki da annobar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China