Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Donald Tusk: Shugabannin EU sun tattauna game da tsarin zaben shugaban hukumar zartaswar kungiyar
2019-05-29 10:36:20        cri
Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Turai ta EU Donald Tusk, ya ce jagororin kasashe mambobin kungiyar ta EU, sun tattauna game da tsarin da za a bi, wajen zaben sabon shugaban kungiyar ba tare da kama sunan wani dan takara ba.

Donald Tusk ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai a jiya Talata, bayan kammala wata liyafar cin abincin dare da aka shiryawa shugabannin.

Ya ce tattaunawar da aka gudanar, ta tabbatar da yarjejeniyar da jagororin suka cimma a watan Fabarairun shekarar da ta gabata, wadda ta bayyana cewa, hukumar zartaswar kungiyar za ta taka rawar da ta dace bisa doka yayin zaben, ba tare da baiwa wani dan takara damar zama jagora ba hamayya ba.

Mr. Tusk ya kara da cewa, yarjejeniyar ta bayyana komai filla filla, cewa hukumar zartaswar za ta gabatar, yayin da majalissar Turai za ta zabi wanda zai zamo sabon shugaban kungiyar. Don haka dole ne sabon shugaban da za a zaba, ya zama ya samu goyon bayan mafiya yawa daga mambobin hukumar zartaswar kungiyar, da kuma mambobin majalissar ta Turai. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China