Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Australia za ta yi watsi da siyasantar da batun annoba
2020-05-19 21:21:36        cri
Jiya Litinin, ministar harkokin wajen kasar Australia Marise Payne ta bayyana cewa, kasashe da dama sun nuna goyon baya ga kudurin dake da nasaba da cutar numfashi ta COVID-19, wanda kungiyar tarayyar kasashen Turai ta gabatar, yayin taron kiwon lafiya na duniya, lamarin da ya nuna muhimancin "binciken kasa da kasa mai zaman kansa" da kasar Australia ta gabatar.

Dangane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Talata cewa, daftarin yaki da cutar COVID-19 da ake tattaunawa a kai a yayin babban taron kiwon lafiyar kasa da kasa, ya dace da matsayin kasar Sin, wanda kuma ya nuna ra'ayi daya da kasa da kasa suka cimma. Zhao ya ce ko kadan, hakan ba shi da nasaba da "binciken kasa da kasa mai zaman kansa" da kasar Australia ta gabatar.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon baya a yi bincike bisa dukkan fannoni, kan ayyukan fuskantar annobar na kasa da kasa, bayan aka cimma nasarar dakile yaduwar ta cikin kasashen duniya. Kuma Sin na bukatar gudanar da wannan aiki bisa jagorancin hukumar WHO, da kuma ka'idar adalci. Wannan shi ne matsayin da kasar Sin take tsayawa kan sa a ko da yaushe. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China