Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi Jinping ya yi kira da a raya makomar bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya
2020-05-19 12:36:25        cri

A daren jiya Litinin 18 ga wata agogon Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin bikin bude babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 73, wanda aka yi ta kafar bidiyo sakamakon bullar cutar COVID-19. Inda Shugaba Xi ya jaddada cewa, annobar cutar COVID-19, ta kasance lamarin ba zato mafi muni da ya shafi lafiyar al'ummar duk duniya tun bayan karshen yakin duniya na biyu, a don haka, ya kamata al'ummomin kasa da kasa su nuna jarumtaka da taimakawa juna domin haye wahalhalu tare. Xi ya kara da cewa, a halin yanzu, ya kamata a kara zage damtse wajen rigakafi da dakile yaduwar cutar, da yada muhimmancin jagorancin hukumar WHO, da kara taimaka wa kasashen Afirka, da kyautata ayyukan tafiyar da harkokin kiwon lafiyar duniya, da dawo da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da ma inganta hadin gwiwar kasa da kasa.

Cikin jawabin da ya gabatar, Shugaba Xi ya jaddada cewa,

"Babban taron kiwon lafiyar duniya na da muhimmanci matuka, yayin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19. Wannan cutar da ta bulla ba zato ba tsammani ta riga ta addabi kasashe da yankuna fiye da 210, da ma mutane fiye da biliyan 7, sannan ta hallaka mutane fiye da dubu 300. A nan ina son na yi amfani da wannan dama wajen mika ta'aziyya ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya, da ma taya iyalansu bakin ciki."

Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya nuna cewa, kwayoyin cuta ba su bambanta kasashe ko kabilu. A yayin da ake fama da annobar cutar COVID-19 mai saurin yaduwa, al'ummomin kasa da kasa sun nuna jarumtaka da taimakawa juna, lamarin da ya nuna kaunar da ke tsakanin jama'a, har ya kasance babban karfi na yaki da cutar. Xi ya jaddada cewa,

"Bayan namijin kokarin da aka yi ba tare da kasala ba, kasar Sin ta samu sauki sosai wajen fama da cutar, kana ta kare lafiyar al'ummarta. Ko da yaushe Sin na martaba ka'idojin fayyace abubuwan da ta sani ba tare da boye komai ba, da ma daukar nauyin da ke wuyanta, kuma ta sanar da WHO da kasashen da abin ya shafa labarin annobar a kan lokaci, da gabatar da yanayin kwayoyin halittar cutar ba tare da bata lokaci ba, har ma ta gabatarwa bangarori daban-daban fasahohinta na rigakafin cutar da jinya wadanda suka kamu da cutar. Hakika kasar Sin ta samar da goyon baya da taimako ga kasashe masu bukata gwargwadon karfinta."

Bugu da kari, Shugaba Xi ya yi kira ga kasa da kasa da su kara mara baya ga WHO a siyasance, da kara samar mata da kudaden da take bukata, a kokarin kara karfin kasashen duniya na ganin bayan cutar. Kana ya yi kira da a kara tallafa wa kasashen Afirka, da kyautata aikin tafiyar da harkokin kiwo lafiyar jama'ar duniya, da kara saurin daukar matakai kan batutuwa na ba zato da suka shafi lafiyar jama'a, da ma raya cibiyar adana kayayyakin rigakafin annoba na duniya da shiyya-shiyya. Haka kuma ya nuna cewa, kasar Sin tana mara baya ga ayyukan tinkarar cutar COVID-19 a duk duniya bayan an kawo karshen cutar, domin takaita fasahohi da gano sassan da ake da nakasu. Amma wannan aiki na bukatar shawarwari na kimiyya, da jagorancin WHO, da ka'idar nuna adalci.

Haka zakila Xi ya gabatar da cewa, ya kamata a daidaita manyan manufofin tattalin arzikin duniya, domin kiyaye aikin tafiyar da masana'antu yadda ya kamata, a kokarin maido da tattalin arzikin duniya nan da nan. Hadin kai shi ne makami mafi karfi wajen samun nasara a kan cutar, kana ita ce hanya mafi dacewa ga al'ummomin kasa da kasa wajen yaki da cutar.

Xi ya sanar da cewa, domin sa kaimi ga hadin kan duk duniya wajen yaki da cutar COVID-19, Sin za ta samar da taimakon kudi dala biliyan 2 nan da shekaru 2 masu zuwa, domin tallafa wa kasashe masu tasowa da cutar ke shafarsu wajen yaki da cutar da ma farfado da tattalin arziki da zamantakewar al'ummarsu. Kana Sin za ta fito da wani tsarin hadin kan asibitoci 30 da ke tsakanin Sin da Afirka, da gaggauta gina babbar hedkwatar cibiyar shawo kan cututtukan Afirka, domin kara karfin Afirka na yaki da cuttuttuka.

A karshe , shugaba Xi ya yi kira da cewa,

"Abu mai muhimmanci, shi ne mu hada kai da juna domin kare rayuka da lafiyar al'ummomin kasashen duniya, da ma kare duniyarmu baki daya, a kokarin raya makomar bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya."

A nasu jawaban, babban sakataren MDD da sauran shugabannin kasashe sun bayyana cewar suna goyon bayan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da muhimmancin jagorancin WHO, baya ga aikin inganta hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da cutar COVID-19.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China