Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi gargadin mayar da martani kan sabbin dokokin Visa da Amurka ta dauka kan 'yan jaridun Sin
2020-05-11 20:55:35        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi gargadin mayar da martani kan sabbin matakan Visa masu tsauri da Amurka ta dauka kan 'yan jaridun kasar ta Sin, inda ta bukaci bangaren Amurka da ta hanzarta gyara kura-kuran da ya yi.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, shi ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai yau Litinin a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya kira sabbin dokokin da Amurka ta fitar a matsayin "rura wutar rikicin siyasa kan kafofin watsa labaran kasar Sin."

A makon da ya gabata ne, kasar Amurka ta fito da wata sabuwar doka, da ta takaita takardun iznin shiga kasar ga manema labarai na kasar Sin na tsawon kwanaki 90, da zabin neman kari, matakin da ya fara aiki Litinin din nan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China