Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude layin jirgin saman dakon kaya da aka tsara tsakanin lardin Hubei da ketare na farko jiya
2020-05-11 20:28:25        cri

Jiya Lahadi 10 ga wannan wata da yamma, da misalin karfe 2 da rabi, wani jirgin saman dakon kaya cike da kayayyaki ya tashi daga filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Tianhe na birnin Wuhan na lardin Hubei domin zuwa birnin Osaka na kasar Japan, wannan shi ne layin kasa da kasa da aka tsara na farko, abin da ke alamta cewa, a hukumance an bude layin jiragen kasa da kasa da aka tsara na farko a lardin tun bayan barkewar annobar COVID-19.

Sakamakon tasirin da annobar ta haifar, an dakatar da daukacin layukan jiragen saman kasa da kasa a filin Tianhe na Wuhan, tun bayan ranar 8 ga watan Aflilun, wato bayan da aka sake bude hanyoyin da suka hada Wuhan da sauran sassan kasar, filin saukar jiragen saman Tianhe na Wuhan ya dukufa kan aikin jigilar kayayyaki domin sassauta matsalolin da kamfanonin lardin ke fuskanta yayin da suke fitar da kayayyaki zuwa ketare, kawo yanzu an riga an fara jigilar kayayyakin da jiragen saman na musamman da aka yi haya daga Wuhan zuwa Los Angeles na Amurka da Melbourne na Australia da Paris na Faransa da Frankfurt na Jamus, ta yadda za a taimakawa al'ummun lardin Hubei domin su dawo bakin aiki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China