2020-05-11 19:43:22 cri |
A cewar Zhao, a safiyar yau Litinin 11 ga watan Mayu ne, tawagar lafiya daga kasar Sin ta tashi zuwa kasar Zimbabwe, daga bisani kuma, sauran tawagogin za su bar kasar Sin zuwa kasashen Jamhuriyar demokiradiyar Congo da Aljeriya. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen na Afirka da kayayyakin yaki da wannan annoba bisa ga yanayin yaduwar cutar da ma bukatun kasashen na Afirka, yana mai jaddada hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama'a da kandagarki da hana yaduwar cututtuka, da shiga a dama da ita a yakin da ake yi na ganin bayan wannan annoba baki daya.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China