![]() |
|
2020-05-10 16:40:55 cri |
Yayin da shugaba Xi yake karamin yaro, wato kusan shekaru biyar ko shida da haihuwa, mahaifiyarsa ta goye shi a bayanta, sun je wani dakin sayar da litattafai domin sayen littafin da aka rubuta kan labarin Yue Fei, shahararren jarumin daular Song ta kudu ta kasar Sin, inda ta gaya masa cewa, mahaifiyar Yue Fei ta saba sassaka kalmomi guda hudu masu ma'anar "Bautawa kasa" a bayan jikinsa, har yanzu shugaba Xi bai manta da kalmomin nan hudu ba, har ya mayar da su a matsayin burinsa na tsawon rai.
Xi ya taba bayyana cewa, "Ya dace iyaye su koyarwa yaransu tunanin da'a da hali na gari tun kanana, da haka yara za su girma cikin koshin lafiya, har za su ba da gudummowa ga ci gaban kasa."
Da gaske ne shugaba Xi ya koyi halin bautawa kasa da jama'a daga iyalinsa.
Har kullum shugaba Xi yana maida hankali kan iyali, haka kuma yana kaunar iyalinsa matuka, amma yana shan aiki a ko da yaushe, har bai iya haduwa da iyalinsa ko a lokacin hutu ba.
Yayin bikin bazara na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin na shekarar 2001, mahaifiyarsa Qi Xin ta taba buga waya ga Xi wanda shi ne shugaban jihar Fujian a wancan lokaci, inda ta gaya masa cewa, "Muddin dai ka gudanar da aiki cikin lumana, to mun gamsu sosai, saboda idan ka dukufa kan aiki, sai ka sauke nauyi bisa wuyanka, babu bambanci."
Babu bambanci tsakanin "karamin gida" da "babban gida", wato iyali da kasa, mahaifiyarsa tana fatan danta ya sauke nauyin raya kasa dake bisa wuyansa, saboda ta fahimce shi, kuma ta goyi bayansa.
A don haka, shugaba Xi ya mayar da nufin samar da wadata ga daukacin iyalan kasar Sin a matsayin muradunsa.
A cikin 'yan shekarun da suka gabata, shugaba Xi bai taba mantawa da abun da mahaifiyarsa ta koyar da shi ba, yana dukufa kan aikin bautawa kasa da jama'a.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China