Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Obama ya soki gwamnatin Trump game da yaki da COVID-19
2020-05-10 16:54:50        cri
Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya soki matakan da gwamnatin Amurka mai ci ke dauka wajen tafiyar da aikin yaki da annobar COVID-19.

A cikin wasu bayanan murya da aka nada na Obama, a wata hira da aka yi da shi a ranar Juma'a, wanda shafin labarai na yanar gizo na Yahoo ya watsa, ya nuna cewa, tsohon shugaban na Amurka ya bayyana shugaba Trump a matsayin mutum mai son kansa, da nuna kabilanci, da kawo rarrabuwar kawuna da haifar da rikici. Ya ce Trump ya mayar da Amurka a matsayin matattarar annobar COVID-19, inda cutar ta fi kamari a duniya.

Obama ya ce, abin da suke yaki da shi a tsawon lokaci shi ne an shafe lokaci mai tsawo ana ta nuna banbancin kabila, da haifar da rarrabuwar kan jama'a, da kuma daukar sauran mutane a matsayin makiya, wannan shi ne al'amari mafi girma game da rayuwar Amurkawa. Ya ce wadannan dalilai ne suka haddasa hatta yaki da annobar a sassan duniya ke fuskantar koma baya.

Obama ya ci gaba da cewa, "Al'amarin annobar ka iya zama mai muni ko da kuwa gwamnati mai inganci ce. Saboda tsananin illolin annobar, amma ni a gani na har da ma abin da ko wane mutum zai iya fada, gwamnatinmu za ta iya taka rawar gani idan da a ce ta yi abind a ya dace."(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China