Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani likitan Faransa: Cutar COVID-19 ta bulla a kasar tun karshen watan Disambar bara
2020-05-04 20:40:55        cri

Jiya Lahadin bisa agogon wurin, wani jami'in kula da marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali a kasar Faransa, ya bayyana cewa, a kalla tun daga karshen watan Disamba na shekarar da ta wuce ne, aka riga aka samu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a kasar.

Furofesan mai suna Yves Cohen, jami'i ne na sashen marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali, a asibitoci guda biyu dake dab da birnin Paris. A cikin wani shiri da aka watsa ta gidan talibijin a wannan rana, ya bayyana cewa, asibitocin biyu sun sake yin bincike kan samfur, na wadanda suka kamu da ciwon numfashi a tsakanin watan Disamban na bara, zuwa watan Janairun na bana.

Bayan binciken da aka yi kan samfur guda 24, an gano cewa, daya daga cikinsu wanda aka kwantar da shi a asibiti a ranar 27 ga watan Disamban bara ya kamu da cutar COVID-19.

A ranar 24 ga watan Janairu ne, kasar Faransa ta sanar da samun wanda ya kamu da cutar a karon farko. Don haka, bisa kalmomin furofesa Cohen, wannan cuta ta bulla a kasar, kimanin wata guda gabanin bayyana hakan a hukumance. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China