Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutumin da aka tabbatar shi ne ya riga saura kamuwa da cutar COVID-19 a Faransa ya fito fili
2020-05-06 12:07:49        cri
Kwanan baya, an mai da hankali sosai kan labarin dake cewar, an tabbatar da wani da ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a karshen watan Disamba na shekarar 2019 a kasar Faransa. A jiya Talata, wannan mutum ya fito, kuma ya yi bayani ga kafofin watsa labarai kan yadda ya kamu da cutar da kuma samun jinya. Bisa labarin da aka samu, an ce, wannan mutum mai shekaru 43, wadda aka haife shi a kasar Algeria, yana zaune a kasar Faransa na shekaru da dama, yana harkokin sayar da kifi, kuma ziyara ta karshe da ya kai a kasar waje ita ce ziyararsa a kasar Algeria a watan Agusta na shekarar 2019.

Sabo da wannan mutum, an canja lokacin tabbatar da wanda ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 na farko daga ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2020 zuwa karshen watan Disamba na shekarar 2019, wanda ya yi wata guda da wuri. A halin yanzu, tawagar likitanci mai ba da jinya ga wannan mutum ba ta iya tabbatar da yaushe da kuma a ina ya kamu da cutar ba, shi ya sa, ba ta iya tabbatar da ko shi ne mutum na farko da ya kamu da cutar ba. A sa'i daya kuma, tawagar ta yi kira ga asibitoci a sauran wuraren kasar Faransa da su sake gudanar da bincike kan samfurorin cutar numfashi da ba su tabbatar da irinsu ba, wadanda suka samu tun lokacin sanyi na bara. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China