Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Putin da Trump sun tattauna ta wayar tarho kan yaki da COVID-19 da nasarar yakin duniya
2020-05-08 10:54:13        cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da takwaransa na Amurka Donald Trump, sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yaki da annobar COVID-19 kana sun taya juna murna kan cika shekaru 75 da samun nasarar yakin duniya na II a lokacin da suka tattauna ta wayar tarho a ranar Alhamis, fadar Kremlin ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce, tattaunawar shugabannin biyu game da yaki da annobar COVID-19, sun tattauna batun yadda bangarorin biyu za su yi hadin gwiwa kan yaki da annobar.

A cewar sanarwar Amurka ta yi wa Rasha tayin bata taimakon kayayyakin kiwon lafiya.

Kremlin ta sanar da cewa, shugabannin biyu sun taya juna murna cika shekaru 75 na samun nasarar yakin duniya II, inda suka jaddada muhimmancin hadin gwiwa a wancan lokacin.

Putin da Trump sun amince da cewa kasashen biyu za su iya cimma nasarori kan batutuwa masu yawa a halin yanzu idan suka bi wannan tsari, wanda ya kunshi dabarun tabbatar da zaman lafiya, da yaki da ayyukan ta'addanci, da warware matsalolin dake shafar aikin yaki da annobar ta COVID-19 a kasashen su. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China