Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin: An yi zabi tsakanin karya da gaskiya
2020-05-06 21:27:49        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, duk da cewa wasu 'yan siyasar Amurka sun yi ta shafa wa kasar Sin kashin kaji, don cimma muradunsu na siyasa a cikin gida, amma kasashen da abin ya shafa sun yi zabinsu a tsakanin karya da gaskiya.

A labarin da aka bayar, Amurka na kokarin matsa wa kawayenta, inda ta bukace su da su tsaya tare da ita, kan "tabbatar da wadanda ya kamata su dauki nauyin yaduwar annobar COVID-19".

A game da tambayar da ta shafi wannan, madam Hua Chunying ta jaddada cewa, ba kawai Amurka na matsawa kawayenta ba ne, har ma tana matsawa sauran kasashen duniya da su kyamaci kasar Sin, da kuma dora laifin yaduwar cutar COVID-19 a kan kasar Sin. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China