Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar tsaron kasar Sudan ta yi Allah wadai da yunkurin hallaka firaministan kasar
2020-03-10 10:12:18        cri

Majalisar tsaron kasar Sudan ta yi Allah wadai da yunkurin kashe firaministan kasar Abdalla Hamdok, majalisar ta tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa.

Bayan wani taron da ta gudanar a Khartoum, majalisar ta bayyana yunkurin hallaka firaministan a matsayin mummunan laifi na neman jefa kasar Sudan cikin hadari a matakin kasa da shiyya da kuma matakin kasa da kasa.

Majalisar ta jaddada cewa dukkan hukumomin kasar sun hada kai da juna domin kalubalantar duk wani yunkuri na wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar Sudan da neman lahanta moriyar jama'ar kasar ta Sudan.

Tun da farko a wannan rana, Hamdok ya tsallake rijiya da baya a yunkurin hallaka shi da aka yi a lokacin da ayarin motocin da yake ciki suka wuce da wani wajen da aka shirya harin bom cikin wata mota a kofar shiga gadar sojojin Sudan dake Khartoum, babban birnin kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China