Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar jamian lafiyar kasar Sin sun kammala aiki a Bukina Faso
2020-05-01 16:30:46        cri

A jiya Alhamis, tawagar jami'an lafiya da kasar Sin ta aike zuwa kasar Burkina Faso ta kammala ayyukanta na raba fasahohin kasar Sin ga takwarorinsu na Burkina Faso, da shirya wasu taruka don horos da ma'aikatan lafiyar kasar, gami da taimakawa kasar tsara ayyukan dakile yaduwar cutar COVID-19.

A ranar 16 ga watan Afrilun da ya gabata ne bisa gayyatar da aka yi musu, wadannan kwararrun ma'aikatan lafiya na kasar Sin suka isa kasar Burkina Faso. Ayyukan da suka gudanar a kasar sun hada da musayar fasahohi tare da kwararrunsu na kasar Burkina Faso masu kula da aikin dakile yaduwar annoba, da binciken yanayin yaduwar cutar COVID-19 a kasar, gami da matakan kandagarki a kasar. Ban da wannan kuma, sun ziyarci wasu manyan asibitocin kasar, don neman sanin yanayin da ake ciki a kasar a fannin shawo kan cututtuka, sa'an nan bisa sakamakon binciken da suka yi, kwararru na kasar Sin sun kira jerin tarukan horaswa a fannonin gano mutanen da suke da yiwuwar kamuwa da cuta, da tsabtace muhalli, da kebe wani sashen jinyar masu fama da zazzabi a cikin asibitoci, da kula da majiyyata masu kamuwa da COVID-19, gami da hana yaduwar cutar a cikin asibitoci, da dai makamantansu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China