Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta bukaci duniya ta kara kaimin yaki da maleriya yayin da ake yaki da cutar COVID-19
2020-04-26 16:50:42        cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bukaci kasashen duniya su kara daukar matakan riga kafin zazzabin maleriya duk da cewa nahiyar Afrika ta mayar da hankali kan yaki da annobar COVID-19.

Kenyatta ya bukaci shugabannin kasashen duniya da cewa kada su kawar da kai wajen cigaba da yin hadin gwiwar yaki da sauran cutukan dake hallaka rayukan bil adama a sassan duniya.

Ya ce ranar Maleriya ta duniya tana kara baiwa alummar kasa da kasa damar yin nazari kan irin nasarorin da aka cimma a yaki da cutar, duk da cewa gwamnatoci na ci gaba da aiwatar da matakan kawo karshen cutar a nahiyar Afrika nan da shekarar 2030.

Ya ce, a kasar Kenya, gwamnatinsa ta yi matukar rage yaduwar cutar daga adadi mafi girma na masu kamuwa da cutar daga miliyan 6 zuwa miliyan 4.6 a cikin shekaru 10 da suka gabata. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China