Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu fama da COVID-19 a Afrika ya zarce 31,933
2020-04-28 12:01:13        cri
Alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afrika, sun nuna cewa, yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar, ya kai 1,423, yayin da na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 31,933 ya zuwa jiya Litinin.

Cikin sabon rahoton da ta fitar kan yanayin cutar a jiya, cibiyar Africa CDC ta ce an tabbatar da bullar cutar a kasashen nahiyar 52.

Ta kara da cewa, ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, mutane 9,566 sun warke daga cutar a fadin nahiyar.

Yayin da ake tsaka da fama da bazuwar cutar a fadin nahiyar, alkaluman cibiyar sun nuna cewa, wuraren da cutar ta fi Kamari sun hada da Afrika ta kudu dake da mutane 4,546 da suka harbu, sai Masar dake da mutane 4534, sai Morocco mai mutane 4,065 yayin da Algeria ke da jimilar mutane 3,382 da aka suka harbu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China