Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan kasuwan kasashen waje na sa ran ganin ci gaban tattalin arzikin Sin
2020-05-01 16:09:05        cri
Wakilin CRI ya yi hira da wasu 'yan kasuwan kasashen waje, wadanda su da kamfanoninsu ke son halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin, da ake sa ran gudanar da shi a shekarar da muke ciki, inda manyan 'yan kasuwan dukkansu suna da karfin gwiwa kan cewar tattalin arzikin kasar Sin na da makoma mai haske.

A hirar da aka yi da Michiaki Oguri, shugaban kamfanin JETRO na kasar Japan reshen birnin Shanghai, ya ce a bara akwai kamfanonin kasar Japan kimanin 200 da suka halarci bikin bajekolin da ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin a duk shekara. Sa'an nan ya ce a bana za a samu karin kamfanonin kasarsa wadanda za su zo kasar Sin don tallata kayayyakinsu.

A nasa bangare, shugaban kamfanin IKEA na kasar Sweden reshen kasar Sin, mista Stephan Deville, ya ce yana da cikakken imani kan cewar kasar Sin za ta farfado daga annobar COVID-19 cikin sauri. Don haka har yanzu kamfaninsa na kokarin bude wasu sabbin kantunansa guda 2 a kasar ta Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China