Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin ya musunta laifin da ake neman dorawa kasar
2020-04-30 21:14:44        cri
A yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya musunta maganganun wasu kasashe, na zargin kasar Sin da kasa daukar matakai masu dacewa a farkon barkewar cutar COVID-19, inda kakakin ya ce wannan zargi ya sabawa gaskiya, kuma wulakanci ne ga jama'ar kasar Sin, wadanda suka yi iyakacin kokari, da sadaukarwa don hana yaduwar cutar.

Dangane da maganar da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya fada kuwa, don neman matsawa kasar Sin lamba ta yarda da wani bincike, kan cibiyar nazarin kwayoyin cuta ta birnin Wuhan, mista Geng Shuang ya bukaci dan siyasar na kasar Amurka, da ya daina yunkurin dora wa kasar Sin laifi.

Ban da wannan kuma, game da tasirin da annobar COVID-19 ka iya haifarwa ga tsaron abinci na duniya, Geng ya ce kasar Sin za ta kara hadin kai tare da sauran bangarorin duniya, don tabbatar da tsaron abinci a duniya baki daya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China