Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwajin kwayoyin jini masu kara garkuwa (Antibody) ya nuna yiwuwar mutane miliyan 2.7 sun kamu da COVID-19 a jihar NewYork ta Amurka
2020-04-24 11:57:55        cri
Gwajin kwayoyin jini masu kara garkuwar jiki wato Antibody, wanda aka yi a jihar New York ta Amurka, ya nuna cewa kaso 13.9 na mutane a jihar, na da karfin garkuwa, wanda ke nufin akwai yiwuwar mutane kusan miliyan 2.7 sun kamu da cutar COVID-19.

Gwamnan jihar New York, Andrewa Cuomo, ya bayyana a jiya cewa, gwajin wanda ma'aikatar lafiya ta jihar ta fara a farkon wannan makon, ya karbi samfurin jini na mutane 3,000 dake sayayya a manyan shaguna, daga wurare 40 na yankuna 19 dake jihar.

A cewar alkaluman jami'ar Johns Hopkins, sakamako na farko-farko, ya nuna cewa ainihin adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar mai mutum miliayn 19.45 ka iya rubanyawa sau 10, fiye da wanda aka fitar a hukumance, wanda ya tsaya kan 263, 754 ya zuwa karfe 2 na yammacin jiya agogon jihar.

Mutanen da sakamakon ya nuna suna da karfin garkuwa, mutane ne da suka kamu da cutar amma suka warke. Gwajin na bada damar tantance yanayin cutar a fadin jihar, sannan yana zaman babban ma'aunin lokaci da kuma yadda za a farfado da harkokin tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China