Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar yada labarai ta Amurka: Amurka wata kasa ce marar dattaku
2020-04-26 17:15:45        cri

Marubuci George Packer ya wallafa wani bayani a mujallar "The Atlantic" mai taken "Muna rayuwa a cikin wata kasa marar dattaku", don bayyana yadda al'ummar Amurka ke tabarbarewa sakamakon COVID-19.

George Packer ya zargi gwamnatin Amurka cewa, ba ta dauki matakai a kan lokaci ba, kuma shugabannin kasar ba su dauki matakai da suka dace ba ko kuma sun yi biris da wannan matsala, har ma wasu suna dora laifi ga saura tare da baza jita-jita da karairayi.

Bayanin ya nuna cewa, abubuwan da suka jefa al'ummar Amurka cikin mawuyacin hali su ne 'yan siyasa masu cin hanci da karbar rashawa, da tsare-tsaren siyasa maras kyau, da kuma manufofin tattalin arizki maras inganci kuma jama'a da bu su san hakikanin halin da suke ciki ba.

Kaza lika ya bayyana cewa, kamata ya yi Amurka ta farfado da kuma sake gina zaman doka da oda a kasar yayin da take kokarin tinkarar wannan mummunar cutar, idan ba haka ba, Amurkawa ba za su iya samun farfadowa daga wannan kalubale ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China