2020-04-25 20:48:08 cri |
Kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci jami'ar Jiaotong ta Xi'an, inda ya bukaci malamai da daliban jami'ar su koyi hali na gari na tsoffin malaman jami'ar, haka kuma su taka rawa a sabon zamanin da ake ciki.
Shugaba Xi ya ce, muhimmiyar ma'anar kaura daga Shanghai zuwa Xi'an ita ce kishin kasa, shi ne kuma dalilin da ya sa kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri a cikin shekaru sama da goma da suka gabata.
Yanzu haka ana yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, hali na gari yana kara karfafa wa ma'aikatan jinya da daliban da suka kammala karatu daga jami'o'i da kuma sauran al'ummun kasar zuciya yayin da suke fuskantar kalubalen. Kamar yadda babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana, ma'aikatan jinya dake cikin asibitocin kasar Sin jarumai ne na gaske, saboda sun shirya sadaukar da rayukansu domin tabbatar da tsaron duniya.
A daya bangaren, yayin da ake yaki da talauci, halin na garin yana karfafa wa al'ummun kasar Sin gwiwa, har ya sa kasar Sin ta cimma burin kubutar da matalauta sama da miliyan 800 daga kangin talauci a cikin shekaru 70 da suka gabata, wato tun bayan da aka kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949.
Yanzu annobar tana ci gaba yaduwa cikin sauri a fadin duniya, har ta gurgunta ci gaban tattalin arziki, a don haka, shugaba Xi ya sake nanata halin na gari na kaura daga yanki mai ci gaba zuwa yanki mai tasowa, domin tunatar da al'ummun kasar cewa, dole ne a kara yin kokari domin samun nasara ta karshe, a sa'i daya kuma, zai ingiza kasar ta cimma muradun ci gabanta na bana bisa shirin da aka tsara, tare kuma da gina zaman takewar al'umma mai matsakaicin wadata a kasar daga duk fannoni.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China