Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi rangadi a lardin Zhejiang kan yadda ake gudanar da harkokin zaman al'umma
2020-04-03 15:02:50        cri

"Kamata ya yi a ci gaba da maida hankali kan aikin kandagarkin cutar, kada a yi taruwa da yawa, matakin da ya zama wani alama ce kan karfin daidaita harkokin kasar. Dole ne a dauki matakin takaita ko sassauci bisa halin da ake ciki." Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wannan furuci ne yayin da ya yi rangadi a lardin Zhejiang kwanan baya, game da aikin kandagarkin cutar COVID-19 da raya tattalin arzikin al'umma.

Wannan cuta dake dabaibaye kasar Sin, annoba ce mafi saurin yaduwa da ta kawo illa ga yankuna mafi yawa, wadda akwai matukar wuya wajen magance ta, tun kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma ta zama wani kalubale ne ga tsari da kuma karfin daidaita ayyukan kasar Sin. An lura cewa, tun bayan bullowar wannan cutar, Sin ta ba da tabbaci ga tafiyar da harkokin kasa yadda ya kamata bisa tsarin yaki da kuma kandagarkin cutar cikin hadin kai da aka kafa a wurare daban-daban. Abin da ya bayyana karuwar karfin kasar Sin na daidaita harkokin al'umma.

Darektan hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta WHO Bruce Aylward ya yabawa matakan da shugabannin kasar Sin suka dauka da kuma hadin kan duk al'ummar Sinawa baki daya bayan ya ganewa idonsa yadda ake kandagarkin cutar a kasar Sin, har ya ce, irin wannan hadin kai da Sinawa suke yi akwai inganci kwarai.

Masanin jami'ar Stanford Ravi Veriah Jacques ya rubuta wani bayani kwanan baya cewa, yadda Sin ta magance COVID-19 ya shaida karfin kasar Sin matuka.

A hakika dai, wannan annoba dake addabar duk fadin duniya ta baiwa duniya wata dama wajen sake kimanta tsare-tsaren kasar Sin da kuma karfin kasar Sin wajen daidaita harkokin al'umma Ya ce, shugaban kasar Sin ya taba bayyana cewa, tsare-tsare da kuma manufofi na samun kyautatuwa a ko da yaushe, shi ma aikin zamanintar da karfin daidaita harkokin kasa na bin salo iri daya, ba wanda zai iya gina birnin Rome cikin yini daya, kuma ba wanda zai tsaya kan wani ci gaba da ya samu ba. Matakin da Sin take dauka na fuskantar matsala kai tsaye da karfin yin kwaskwarima, su ne abubuwa mafi muhimmanci a cikin tsarin daidaita harkokin kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China