Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Rangadin aikin da Shugaba Xi Jinping ya yi a lardin Shaanxi ya nuna imanin kasar Sin na cimma burin kau da talauci daga dukkan fannoni
2020-04-24 00:07:15        cri

"Ina da imanin cewa, kasar Sin za ta iya cimma burin kawar da talauci daga dukkan fannoni bisa shirin da muka tsara." Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fadi hakan ne yayin da yake yin rangadin aiki a wata unguwar gundumar Pingli da ke lardin Shaanxi. Kuma wannan shi ne karo na shida da Shugaba Xi ya je kananan wurare don rangadin aiki.

Bisa shirin da aka tsara, Sin za ta kammala aikin kau da fatara a bana, ta yadda za a iya samun zamantakewar al'umma mai wadata daga dukkan fannoni. Amma Cutar COVID-19 da ta bulla ba zata ta kara wahalar cimma wannam babban burin. Ya zuwa yanzu ma dai, sauran kwanaki sama da 200 kawai sun rage, shin kasar Sin za ta iya cimma burinta ko a'a? Lamarin da ya jawo hankalin duniya sosai.

Yayin da Xi ke yin rangadin aiki a Shaanxi daga ranar 20 zuwa ranar 23 ga wata, ya ba da jagoranci ga yadda za a dauki matakan ba da taimako a fannonin masana'antu, samar da guraban aikin yi, kiwon lafiya, ba da ilmi don yaki da talauci, lamarin da ya ba da sakon cewa, Sin za ta iya kammala aikin kau da talauci a kan lokaci. Wanda kuma ya nuna manufar Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta mai da jama'a a gaban komai.

Wuraren da Xi ya zaba a wannan ziyararsa na da babbar ma'ana. A yammacin ranar 20 da ma safiyar ranar 21 ga wata, ya je gundumar Zhashui da gundumar Pingli da ke yankin Qinba da ke kan duwatsu don rangadin aiki. Yankin kuwa ya kasance wuri ne da ya fi fama da fatara. Don haka, ana iya gano cewa, ziyarar Xi ya nuna kudurin kasar Sin na cimma burin kawar da talauci daga dukkan yankunan kasar komen wahalar da za ta sha.

Ban da wannan kuma, Shugaba Xi ya ba da umurni ga ayyukan yaki da talauci na nan gaba, inda ya jaddada cewa, ya kamata a dauki matakai masu dacewa bisa halin da ake ciki, da ma gudanar da ayyukan fitar da masu fama da talauci daga kangin talauci, da kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu a fannin yaki da talauci, wadanda suka hada da raya sana'o'in musamman da ke dace da yanayin da ake ciki, da kafa tsarin sanya ido kan ayyukan fama da talauci don magance a sake shiga yanayin talauci, da ma ci gaba da samar da goyon baya ga aikin kauratar da mutane masu fama da talauci da dai sauransu.

Ta haka, ana iya gano cewa, wadannan matakai na yin la'akari da yanayin da ke ciki yanzu, baya ga yin hangen nesa, don haka ba ma kawai zai taimaka wa kasar Sin wajen rage illar da cutar COVID-19 ke haddasawa, har ma zai tabbatar da wadanda suka fita daga talauci ba za su sake fama da talaucin ba.

Yadda shugaban kasar Sin ya yi rangadin aiki a Shaanxi a wannan muhimmin lokaci, babu shakka zai karfafa zukatan al'ummar Sin wajen cimma burin kawar da talauci daga dukkan fannoni, baya ga kara karfin gwiwarsu wajen kawo kwashen matsalar fama da talauci wanda ke damunsu har na tsawon shekaru fiye da dubu. (Kande Gao, ma'aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China