Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar Xi A Zhejiang Ta Sa Kaimi Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Sin
2020-04-01 21:47:26        cri
A ranar 29 ga watan jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci wani kamfanin kera na'urori a birnin Ningbo na lardin Zhejiang, inda ya bayyana cewa, yanzu ana kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, a don haka dole ne a tabbatar da lafiyar ma'aikata yayin da ake kokarin dawo wa bakin aiki.

Wannan ne karo na hudu da shugaba Xi ya kai rangadin aiki tun bayan da kasar Sin ta fara yaki da annobar, kana karo na biyu da ya gudanar da rangadin aiki a wajen birnin Beijing. Yayin rangadin aikinsa a lardin Zhejiang, da farko ya ziyarci tashar ruwan tekun Zhoushan na birnin Ningbo, inda adadin kayayyakin da aka yi jigilar su a bara ya kai tan biliyan 1 da miliyan 120, inda ya kai matsayin koli a duniya a cikin shekaru 11 da suka gabata, daga baya ya je yankin masana'antun kera kayayyakin motoci na Daqi dake unguwar Beilun ta birnin Ningbo, inda kanana da matsakaitan kamfanoni masu zaman kansu ke cunkushe, a bayyane an lura, wuraren biyu da shugaba Xi ya ziyarta wurare ne da suka fi rinjaye a bangaren bude kofa ga waje.

Yayin taron shugabannin kungiyar G20 da aka kira a ranar 26 ga watan jiya, an gabatar da cewa, kasashen duniya za su hada kai domin kare jerin ayyukan masana'atu a fadin duniya, ya zuwa ranar 27 ga wata, an yi nuni a gun taron hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS cewa, kasar Sin za ta hanzarta fito da tsarin samar da kayayyaki tsakanin kasa da kasa, yanzu haka shugaba Xi ya jaddada a birnin Ningbo cewa, kasar Sin za ta yi kokari domin tabbatar da cewa, an shigo tare da fitar da kayayyaki daga ketare, duk wadannan sun nuna cewa, kasar Sin tana sauke nauyi a matsayinta na babbar kasa a duniya.

Yayin ziyararsa a lardin Zhejiang, shugaba Xi ya ce, duk da cewa kamfanonin kasar Sin sun gamu da matsala yayin da ake yaki da annobar COVID-19, amma gwamnatin kasar ta fito da wasu matakan da suka dace domin taimakawa kamfanoni matsakaita da kanana, ta yadda za su fita daga mawuyacin yanayi, haka kuma za a ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba yadda ya kamata.

A yau Laraba bayan da shugaba Xi ya saurari rahoton aikin lardin Zhejiang, ya bayyana cewa, har kullum damar samun ci gaba tana kasancewa da rikici, muddin aka kawar duk wata matsala, za a samu damar ci gaba, tsokacinsa ya karfafa imanin al'ummun kasar kan makomar tattalin arzikin kasar ta Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China