Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakofin watsa labaran Amurka sun tono jita-jitar asalin kwayar cutar COVID-19
2020-04-25 16:56:28        cri
Kwanan baya tashar yanar gizo mai zaman kanta ta Grayzone ta Amurka ta wallafa wani rahoto mai taken "Yadda Trump ya baza jita-jitar wai COVID-19 ta samo asali daga dakin gwajin kasar Sin", inda ta tono yadda 'yan jarida masu sassaucin ra'ayi da gwamnatin Amurka suka baza jita-jitar.

Rahoton ya bayyana cewa, matakin da aka dauka ya yi kama da yadda gwamnatin George Bush ta yada jita-jitar wai kasar Iraki ta mallaki makaman kare dangi. A karshen watan Janairun bana, jaridar Washington Times ta fitar da labarin kanzon kurege na farko game da COVID-19 ta samu asali daga dakin gwajin birnin Wuhan na kasar Sin. A kwanakin baya jaridar The Washington Post ta wallawa wani sabon labarin da Josh Rogin ya rubuta. Hakika a shekarun baya, gwamnatin Bush ta yi hadin gwiwa da 'dan jarida Judith Miller, domin gabatar da labarin jabu, na wai Iraki ta kera makaman kare dangi, a sanadin haka, yaki ya barke, inda sojojin Amurka sama da dubu goma da mutanen Iraki masu yawan gaske suka rasa rayukansu.

A ranar 14 ga watan Aflilun da muke ciki, jaridar The Washington Post ta wallafa rahoton marubuci Josh Rogin mai taken "Gargadin ma'aikatar harkokin wajen Amurka kan matsalar tsaron dakin gwajin kwayar cutar Corona ta dabbar Jemage na birnin Wuhan",inda ya bayyana cewa, ya samu sakon da ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sin ya aika a watan Janairun shekarar 2018, a cikin sakon, an rubuta cewa, ana gudanar da nazari kan yadda za a yada kwayar cutar Corona ta Jemage zuwa ga bil Adama a dakin gwajin Wuhan, lamarin da ya nuna cewa, kila annoba mai tsanani kamar SARS za ta barke.

Tashar yanar gizon Grayzone ta yi nuni da cewa, ya rubuta rahoton ne gwargwadon takadar gwamnatin da jami'an Amurka suka gabatar domin matsawa kasar Sin lamba, daga baya 'yan siyasar Amurka suka fara daukar matakan shafawa kasar Sin bakin fenti daga duk fannoni.

A ranar 17 ga wata, sakataren harkokin wajen Amurka Pompeo ya bukaci gwamnatin kasar Sin da ta amince da gudanar da bincike kan cibiyar nazarin kwayar cuta ta Wuhan.

Kana shugaban kasar Donald Trump ya sanar da cewa, akwai dalilin da sa aka amince cewa, an kirkira kwayar cutar COVID-19 ne a cikin dakin gwajin kwayar cuta dake Wuhan.

Grayzone ya yi nuni da cewa, yanzu watanni shida suka rage kafin babban zaben Amurka, amma kasar tana cikin mawuyancin yanayi, lamarin da ya sa Trump ke dora laifi kan wasu ta hanyar baza jita-jita.

Grayzone ya kara da cewa, ainihin manufar jami'in ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sin na aika sakon shi ne, domin jaddada cewa, nazarin dakin gwajin Wuhan yana da ma'ana, kila zai yi hasashe ko riga kafi kan barkewar kwayar cutar Corona.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China