Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karar da 'yan siyasar Amurka suka kai Sin wasa ne domin yunkurin dora laifi kan wasu
2020-04-24 21:07:26        cri
A halin yanzu, annobar cutar COVID-19 tana yaduwa cikin sauri a cikin kasar Amurka, a sanadin hakan, wasu Amurkawa sun damu matuka, har sun dauki mataki na kai karar kasar Sin, da nufin neman kudin diyya.

Baya ga babban mai gabatar da kara na jihar Missouri Eric Schmittm, yanzu haka ma takwaransa na jihar Mississippi Lynn Fitch, shi ma ya gabatar da irin wannan kara ta gwamnatin kasar Sin a ranar 22 ga wata, agogon jihar, inda ya gabatar da rokon neman kudin diyya. Hakika wadannan kararraki ba su da tushen doka ko kadan, kuma wani wasa ne kawai da suke yi domin dora laifi ga wasu.

Da farko dai, bisa ka'idar diplomasiyya, kotun wata kasa ba za ta iya sauraron kara kan wata kasa daban, ko gwamnatin wata kasar daban da dukiyarsu ba. Kana tun daga ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2019, lokacin da wani asibitin lardin Hubei na kasar Sin ya gabatar da rahoto game da majinyata guda uku, wadanda suka kamu da cutar huhu ba tare da gano ainihin dalili ba, kuma a ranar 31 ga watan Disambar bara, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rahoto ga ofishin hukumar lafiya ta duniya dake kasar Sin, ya zuwa ranar 3 watan Janairun bana, an kammala aikin gabatar da rahoton a hukumance, daga baya kasar Sin ta tace kwayar cutar COVID-19 cikin nasara a ranar 7 ga watan Janairu, kuma ta raba sakamakon tantance kwayar cutar tare da hukumar ta WHO a ranar 12 ga watan Janairu, ta kuma rika sanar da sabbin alkaluman hakan ga kasa da kasa a kowace rana. A zahiri ana iya lura da cewa, kasar Sin ta sauke hakki bisa wuyanta bisa ka'idar kiwon lafiyar kasa da kasa.

Kana babban mai gabatar da kara na jihar Missouri ta Amurka Eric Schmittm, ya gabatar da dalilai biyu marasa tushe, inda ya bayyana jita-jitar cewa, kasar Sin ba ta samar da alkaluman yaduwar annobar cikin kasar ta na gaskiya ba, kuma ya zargi gwamnatin kasar Sin da ajiye kayan rufe baki da hanci, da sauran kayayyakin kandagarkin annobar.

Hakika har kullum kasar Sin tana samar da alkaluman annobar na gaske a fili. Misali tun daga ranar 3 ga watan Janairun bana, kasar Sin ta sanar da bayanai masu nasaba da batun ga Amurka. Ya zuwa ranar 27 ga watan Janairu kuma, jami'an kiwon lafiya na sassan biyu, sun tattauna ta wayar tarho. A ranar 30 ga watan Janairu, hukumar lafiya ta kasar Sin ta gayyaci Amurka, da ta shiga tawagar masanan hukumar lafiya ta duniya a hukumance.

Ya zuwa karshen watan Fabrairu, hadaddiyar tawagar masanan kasar Sin da hukumar lafiya ta duniya wadda ke kunshe da masanan Amurka guda biyu, ta zo kasar Sin domin gudanar da rangadin aiki har na tsawon kwanaki tara, duk wadannan sun nuna cewa, Amurka ta rika samun bayanai masu nasaba da wannan batu kuma a kan lokaci, kana sassan biyu suna gudanar da hadin gwiwar fasaha cikin lumana.

Game da adana kayayyakin kandagarkin annobar da aka zargi kasar Sin kuwa, shi ma zargi ne maras tushe. Bisa kididdigar da hukumar kwastam ta kasar Sin ta yi, an ce, tsakanin ranar 1 ga watan Maris da ranar 17 ga wannan wata, gaba daya kasar Sin ta samarwa Amurka kayan rufe baki da hanci biliyan 1 da miliyan 864, da safar da ake amfani da ita a asibiti miliyan 258, da kayan ba da kariya miliyan 29 da dubu 190, da tabarau iri na ba da kariya miliyan 3 da dubu 130, da na'urar taimakawa numfashin da ake shigarwa ta wuya 156, da na'urar taimakawa numfashin da ake shigar wa ta baki 4254.

Yanzu haka, daukacin bil Adama suna shan wahalar wannan annoba, babu wata kasa ta taba kai karar wata kasa daban, ko wata kabila daban bisa dalilin kiwon lafiyar jama'a a tarihi. Ko shakka babu lamarin zai kara kyamar juna tsakanin al'ummun kasa da kasa, zai kuma jefa su cikin mawuyancin hali mai tsanani. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China