Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ina dalilin da ya sa kamfanonin Amurka suke kara zuba jari a Sin yayin dakile COVID-19?
2020-04-23 20:24:42        cri
A jiya Laraba, an gudanar da bikin kaddamar da aikin samar da sinadarin ethylene, na kamfanin ExxonMobil na Amurka a reshensa dake birnin Huizhou na lardin Guangdong, wanda aka zubawa jarin da yawansa ya kai dala kusan biliyan goma, a biranen Beijing da Huizhou na kasar Sin, da kuma birnin Dallas na Amurka ta kafar bidiyo.

Lokacin kaddamar da aikin ya fi jawo hankalin jama'a, saboda yanzu haka ana fama da yaduwar annobar cutar COVID-19, kuma farashin mai shi ma yana ta yin kasa matuka, amma kamfanin ExxonMobil ya tsai da kudurin zuba jari a kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, wannan babban kamfani yana cike da imani kan kasuwar kasar Sin.

To amma abun tambayar shi ne, ko daga ina ya samu wannan karfin gwiwa? Hakika kasar Sin tana da ingantattun kayayyakin more rayuwar jama'a, tana kuma rika da kudurin kara bude kofa ga ketare, tare kuma da kara kyautata muhallin kasuwanci. Game da kamfanin na ExxonMobil kuwa, daga tsara shirin kafa aikin samar da sinadarin ethylene, zuwa samun rajista daga hukumomin da abun ya shafa na kasar Sin, a karshe dai an kaddamar da aikin cikin watanni 18 kacal, ana kuma iya cewa, kamfanin ya samu imani ne daga "saurin kasar Sin".

An lura cewa, bayan barkewar annobar COVID-19, wasu 'yan siyasar Amurka sun baza jita-jitar cewa, jerin ayyukan samar da kayayyaki tsakanin Sin da Amurka ya gamu da matsala, har ma sun gabatar da shawarar cewa, gwamnatin Amurka ta biya kudi ga kamfanonin kasar domin su janye jiki daga kasar Sin, amma sai ga shi a yanzu an kaddamar da aikin kamfanin Amurka, wanda aka zuba jari kusan dala biliyan goma a kasar Sin, lamarin da ya mayar da martani mai karfi ga waccan jita-jitar.

Kana ana ganin cewa, dalilin da ya sa 'yan kasuwar ketare suke kara zuba jari a kasar Sin shi ne, suna kaunar babbar kasuwar kasar wadda take da al'ummun da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400.

Misali kamfanin ExxonMobil, zai sayar da kayayyakin da zai samar bisa mataki na farko a kasuwar kasar Sin kai tsaye, inda aka yi hasashen zai samu kudin shiga har kudin Sin RMB biliyan 39, kwatankwacin dala biliyan 5.5, kamar yadda wani masanin zuba jari ya bayyana. Ya ce "Kasuwar kasar Sin mafi girma tana cikin gida."

Ko shakka babu tattalin arzikin kasar Sin, zai ci gaba da habaka, haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da kasance wuri mafi jawo hankalin masu zuba jari na kasa da kasa. Nan gaba kuma, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga ketare, kuma tabbas manyan kamfanonin kasa da kasa masu hangen nesa, za su samu karin damammaki a kasar ta Sin. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China