Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar Xi a Shaanxi ta nuna aniyar Sin ta kare halittu da samun ci gaba
2020-04-24 19:22:51        cri
Tun bayan da aka kira babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekarar 2012, har kullum shugaban kasar Xi Jinping yana mai da hankali matuka kan gina wayewar kai game da halittu.

Kwanan baya, shugaba Xi ya yi rangadin aiki a lardin Shaanxi dake yammacin kasar, inda ya ziyarci lambun shan iska na gandun daji na duten Niubeiliang dake tudun Qinling na lardin.

Kafin 'yan shekarun da suka gabata, an taba lalata halittun tudun Qinling ta hanyar gina manyan gidajen kwana ba bisa ka'ida ba a wurin. Game da hakan, shugaba Xi ya taba bukatar yin bincike har sau shida. Ya zuwa shekarar 2018, an rushe manyan gidajen kwana sama da 1000 da aka gina a kan tudun, an kuma hukunta wasu jami'an da suka sa hannu a cikin batun bisa doka, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana daukar tsattsauren matakai domin kare muhallin halittu.

Yanzu haka, Xi ya sake bukatar jami'ai na hukumomi daban daban na lardin Shaanxi, da kada su sake aikata irin wannan laifin lalata halittu, tsokacin na sa ya shaida cewa, shugaba Xi yana ba da muhimmanci sosai kan aikin kare halittu.

Tun daga shekarar 2012, wato bayan da aka kira babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, gwamnatin kasar tana dukufa kan zamanintar da kasar, daga fannoni biyar da suka hada tattalin arziki da siyasa da al'adu da zamantakewar al'umma da wayewar kan halittu, musamman ma tun bayan da aka shiga sabon mataki na samun ci gaba mai inganci. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai rike da mulkin kasar, da gwamnatoci na mataki daban daban na kasar, da daukacin al'ummun kasar suna kara mai da hankali kan aikin kiyaye halittu yayin da suke kokarin yaki da talauci da kuma samun ci gaba.

A shekarar bana da muke ciki, za a kammala aikin kawar da talauci daga duk fannoni a fadin kasar Sin, har ma a gina zamantakewar al'umma mai matsakaicin wadata a kasar, a daidai wannan lokaci, manufar samun ci gaba, tare da kiyaye muhallin da shugaba Xi ya tsara a lardin Shaanxi tana da ma'ana mai zurfi.

Da farko, annobar cutar COVID-19 tana kawo kalubale mai tsanani ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, to amma abun tambaya a nan shi ne, ko kasar Sin za ta canja manufarta ta raya kasa?

Kana ta yaya za a cimma burin kawar da talauci a lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin kafin karshen bana?

Game da tambaya ta farko, shugaba Xi ya ce, ba zai yiwu a kasa kula da aikin kiyaye halittu ba, inda ya jaddada cewa, "Dutse mai launin kore da ruwa mai tsabta, dukiyar halittu ne, su ma kuma dukiyar tattalin arziki ne."

Shugaba Xi ya kara da cewa, "Idan bil Adama sun raya tattalin arziki tare da kiyaye muhalli, tabbas za su ji dadin rayuwa a cikin muhalli mai inganci." Sabon tsokacinsa ya nuna huldar inganci dake tsakanin muhallin halittu da ci gaban tattalin arziki. A sa'i daya kuma, ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta canja muradunta na raya kasa, tare da kiyaye muhalli ba, duk kuwa da yiwuwar gamu da matsala.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China