Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin Amurka kan cibiyar nazarin kwayar cuta ta Wuhan ba shi da tushe
2020-04-21 20:57:46        cri
A ranar 19 ga wata, tashar talibijin ta Fox News dake kasar Amurka, ta gabatar da wani rahoto, game da jita-jitar cewa, wata cibiyar nazarin kwayar cuta dake birnin Wuhan na lardin Hubei dake nan kasar Sin ne asalin kwayar cutar COVID-19. Rahoton ya kuma kara da cewa, Amurka za ta gudanar da bincike kan lamarin daga duk fannoni.

To sai dai kuma a hannu guda, babu wata shaida ko kadan, dake gaskata ra'ayin da aka bayyana a cikin rahoton, sai dai kawai an ce wani masanin dake kyamar kasar Sin ya yi tsokacin cewa, cibiyar ta gaza samar da tabbacin tsaro. Abun tambaya a nan shi ne ta yaya za a iya amincewa da irin wannan rahoto maras tushe?

An lura cewa, a ko da yaushe, tashar talibijin ta Fox News, tana goyon bayan shugabnanin kasar ta Amurka, inda a yanzu haka take siyasantar da annobar COVID-19, dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, tana son dora laifin mahukuntan Amurka kan kasar Sin.

Hakika cibiyar nazarin kwayar cuta ta Wuhan, tana gudanar da hadin gwiwar nazarin kimiyya tsakaninta da masana kimiyya na kasashen Amurka, da Faransa da sauransu. Misali, an gina dakin gwajin ma'aunin tsaron P4 a cibiyar Wuhan, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Faransa, kuma ko shakka babu, an tabbatar da tsaron cibiyar bisa ma'aunin sana'a.

Tun bayan barkewar cutar COVID-19, ma'aikatan cibiyar sun dukufa wajen aikin nazarin kwayar cutar, har ma sun ba da babbar gudumowa ga kasa da kasa, yayin da suke neman samun hanyoyin tantance cutar, tare kuma da hada allurar riga kari.

Kana, kan batun ko an hada kwayar cutar, ko a'a, manyan cibiyoyin nazarin kimiyya na kasa da kasa sun riga sun ba da amsa mai tabbaci. A ranar 18 ga watan Fabrairu, manyan masana kimiyya da yawansu ya kai 27, sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa a mujallar The Lancent, inda suka yi watsi da ra'ayin kirkirar kwayar cutar COVID-19, har ma shahararen masanin nazarin cututtuka masu yaduwa na Amurka Anthony S. Fauci ya bayyana cewa, dabbobi ne suka yada kwayar cutar ga bil Adama, ba kirkirar ta aka yi a cikin dakin gwaji ba.

Yanzu haka dai daukacin bil Adama suna fama da annobar, kuma hadin kai ya fi muhimmanci, idan ana son ganin bayanta, kuma abokiyar gabar Amurka kwayar cutar ce ba kasar Sin ba. Dole ne 'yan siyasar Amurka wadanda suke siyasantar da annobar su kara fahimta cewa, ba za su cimma yunkurinsu na bata sunan kasar Sin ba, kuma dora laifi ga wasu shi ma ba zai iya sassauta yanayi mai wahala, da wannan annoba mai tsanani ke haifarwa a kasarsu ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China