Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tunzurawa da gangan ba zai gurgunta huldar Sin da Afirka ba
2020-04-22 20:58:07        cri
Wata daliba 'yar kasar Tanzaniya dake karatu a kwalejin koyon ilimin likitanci a jami'ar Zhongshan dake birnin Guangzhou na kasar Sin tsawon shekaru shida mai suna Veya, ta ce, idan ana son ganin bayan annobar COVID-19, dole a hada kai, kuma birnin Guangzhou ya zame mata gida da take matukar kauna.

Tsokacin Veya tamkar martani ne mai karfi ga wasu Amurkawa, masu yunkurin lalata huldar dake akwai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wasu Amurkawa sun rika yada jita-jitar cewa, ana nunawa 'yan Afirka dake zaune a birnin Guangzhou raini, inda har ta kai karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Guangzhou, shi ma ya bayyana cewa, an nunawa wasu Amurkawa 'yan asalin kasashen Afirka dake birnin raini.

To sai dai kuma wadannan zarge zarge, an lura cewa yunkuri ne kawai na gurgunta huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A sa'i daya kuma, suna son bata sunan kasar Sin ne, a gabar da take kokarin dakile annobar numfashi ta COVID-19.

Duk da wannan yunkuri na su, ba zai yiwu su iya boye ainihin abubuwan dake kasancewa ba. Yadda kasar Sin take sada zumunta tsakaninta da kasashen Afirka, 'yan uwa al'ummun kasar Sin dake kasashen Afirka su suka fi kowa fahimtar hakan.

Kwanan baya, ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya gaskata cewa, wasu 'yan kasarsa ba su bi ka'idojin da gwamnatin kasar Sin ta tsara game da dakile annobar COVID-19 a birnin Guangzhou ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun gabatar da labarai ba na gaskiya ba.

A daya bangaren kuma, jami'in ma'aikatar yada al'adun Najeriya Ochuku ya yi nuni kai tsaye da cewa, wasu kasashen yamma karkashin jagorancin Amurka, sun harhada wasu hotunan bidiyo, domin yada su a dandalin sada zumunta, wanda hakan ya haifar da rashin fahimta.

Tun bayan barkewar annobar, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labarai na Amurka, sun rika tunzura jama'a domin su kyamaci kasar Sin. Misali sun yi amfani da kalmar "kwayar cutar kasar Sin", da "kwayar cutar Wuhan", haka kuma sun yi suka da cewa, kasar Sin tana da makarkashiyar siyasa, yayin da take samar da tallafin kiwon lafiya ga sauran kasashe, har ma sun yi jita-jitar cewa, kasar Sin tana aiwatar da manufar wariyar kabila a Guangzhou, amma yunkurinsu shi ne, bata sunan kasar Sin, tare kuma da lalata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangaren dakile annobar.

Amma kamar yadda babban daraktan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna, kwayar cutar tana shafar daukacin kasashen duniya, kuma nasarar da za a samu kan cutar, tana dogara ne kan tsarin likitanci na kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen dake fama da talauci mai tsanani.

A don haka hukumar WHO, ta fara gudanar da shirin tallafawa kasashe mafiya shan wahala, domin cimma burin ganin bayan annobar daga duk fannoni a fadin duniya.

Har kullum kasar Sin tana nuna goyon baya ga shirin, tare kuma da samar da hakikanin tallafi a kan lokaci. Misali tana kula da mutanen Afirka dake zaune a kasar, kuma tana samarwa kungiyar tarayyar Afirka, da kasashen Afirka kayayyakin kandagarkin annobar da dama, kana tana more fasahohin yaki da annobar da ta samu tare da su. Ban da haka, ta tura tawagoyin likitoci ga kasashen Afirka, domin kara zurfafa hadin gwiwar kiwon lafiya dake tsakaninsu. Makasudin yin haka shi ne, nuna godiya ga kasashen Afirka, wadanda suka taba samar da tallafi gare ta, yayin da take kokarin dakile annobar. Hakan kuma shi ne zai tabbatar da tsaron lafiyar jama'a a fadin duniya baki daya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China