2020-04-07 13:09:12 cri |
Jiya Litinin, babban direktan kamfanin JPMorgan Chase & Co, Jamie Dimon ya bayyana a cikin wata wasika da ya rubuta ga masu hannun jarin kamfanin cewa, tattalin arzikin Amurka zai fuskanci babban koman baya kamar matsalar hada-hadar kudi da ta barke a shekarar 2008.
Tsohuwar shugabar tsarin tattara kudi na Amurka wato The Fed, Janet L. Yellen, ita ma tana rike da wannan matsayi. Bisa labarin da CNBC ta gabatar, Janet L. Yellen na ganin cewa, jimillar GDPn Amurka a watannin Afrilu da Mayu da kuma Yuni zai ragu a kalla kashi 30%, a cewarta, ana yin hasashe mafi tsanani yanzu.
A jiya Litinin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Dorothea Merkel ta kammala killace kanta, inda ta kira wani taron manema labarai cewa, COVID 19 ta zama jarrabawa mafi tsanani ga EU tun bayan kafuwarta, kuma ta jaddada wajibcin hadin kan kasa da kasa don tinkarar wannan annoba tare.
Ban da wannan kuma, a daren wannan rana, firaminitan kasar Italiya Giuseppe Conte ya ba da jawabi ta telibijin bayan taron ministocin kasar, inda ya sanar da fitar da jerin matakai don tallafawa tattalin arziki a mawuyancin hali, tare kuma da kara sanar da ware kudi Euro biliyan 400 don ba da tabbaci ga kamfanoni da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya kuma nanata cewa, matakan da aka dauka a wannan karo, matakai ne mafi karfi a cikin tarihin kasar wajen tallafawa tattalin arziki. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China