Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka suna mayar da hasarar rayuka gasar siyasa
2020-04-20 20:28:21        cri
A kwanakin baya, sau da dama shugaban kasar Amurka ya rika zargin kasar Sin, yayin taron gabatar da gajeren bayani kan yanayin da kasar ke ciki, a fannin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, wanda yake gudanarwa a fadar shugaban kasa.

Cikin zarge zargen, ya rika bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta bayyana hakikanin adadin mutanen da cutar ta hallaka ba, inda ya kai ga nuna hotunan wasu alkaluman adadin mutanen da suka rasa rayukan su, a cikin mutanen da suka kamu da cutar dubu 100 a cikin kasashe goma, inda ya bayyana cewa, a Amurka, adadin ya kai kaso 11.24, adadin da ya yi kasa da na kasashen Sifaniya da Faransa da Italiya, amma a kasar Sin, adadin bai wuce kaso 0.33 kacal ba. A cewar sa, ba zai yiwu ake hakan ta faru ba.

Kowa yana da rai guda daya ne kacal, ana bakin ciki matuka da ganin hasarar rayuka yayin barkewar annobar, amma wasu 'yan siyasa ba su nuna biyayya, kana ba su kiyaye rayuka, maimakon haka suna mayar da hasarar rayuka a matsayin lambobin kidaya kawai. Ana ganin cewa, wadannan 'yan siyasa ba su da da'a ko kadan, har ta kai ga masu shiga yanar gizo na Amurka na sukar su. Irin wadannan masu suka sun bayyana cewa, "Wannan annoba ba gasar mutuwa ba ce, mutane da dama suna rasa rayukansu."

An lura cewa, yanzu haka yanayin dakile annobar da Amurka ke ciki yana kara tsanani, al'ummun kasar ba su gamsu da gwamnatin kasarsu ba, a don haka manyan jami'an kasar suna shafawa kasar Sin kashin kaji daya bayan daya, domin dora laifi kan kasar Sin, tare kuma da hana ci gabanta.

Hakika yayin da wasu 'yan siyasar Amurka suke gaza kula da tsananin yaduwar annobar COVID-19, a ko da yaushe, mahukuntan gwamnatin kasar Sin suna mayar da rayukan al'ummunta, da lafiyar jikinsu a matakin farko, har ma suna daukar matakan da suka dace cikin gaggawa, inda suka tura likitoci da nas nas sama da dubu 42 zuwa ga lardin Hubei, a sa'i daya kuma, al'ummun kasar da yawansu kai biliyan 1 da miliyan 400 sun killace kansu a cikin gida bisa radin kai.

A karshen watan Maris, mujallar "Science" ta fitar da wani sakamakon nazari, inda aka nuna cewa, a cikin farkon kwanaki 50 bayan barkewar cutar, an rufe birnin Wuhan, matakin da ya hana mutane sama da dubu 710 a sassa daban daban na kasar waje da birnin kamuwa da cutar, a sanadin haka, adadin mutanen da aka killace da za su kamu da cutar a kasar Sin ya ragu da kaso 96 bisa dari. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ta rage mutanen da suka rasa rayuka sakamakon cutar fiye da kima.

An ga gwamnatin Amurka ba ta dauki matakan da suka dace ba a kan lokaci yayin da take dakile annobar, har tana dora laifi kan wasu, idan tana ci gaba da hada annobar da siyasa, tana ci gaba da mayar da hasarar rayuka gasar siyasa, al'ummun kasar Amurkan za su sha wahala. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China