Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta tura tawagar jami'an lafiya na gaggawa ga jahohi 23 da cutar COVID-19 ta shafa
2020-04-23 09:44:50        cri

Gwamnatin Najeriya ta tura tawagar jami'an lafiya masu bada agajin lafiya na gaggawa zuwa jahohi 23 na kasar wadanda annobar COVID-19 ta shafa bayan da aka samu karuwar adadi mafi yawa na masu dauke da cutar a rana guda.

Karamin ministan lafiyar kasar Olorunnimbe Mamora, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Legas, cibiyar kasuwancin kasar, ya ce ana kara samun yaduwar cutar a sauran yankuna sakamakon yadda cutar ke yaduwa a tsakanin jama'a.

Ministan ya ce dabarun da ake bi na binciko masu dauke da cutar a tsakanin jama'a, yana bukatar samar da karin kayayyakin gwaje-gwajen cutar, inda ya jaddada bukatar samar da karin dakunan gwaje-gwaje domin tantance masu kamuwa da cutar.

Ya kara da cewa, akwai matukar wahalar amfani da hanyoyin sadarwa wajen binciko masu dauke da cutar a yankunan karkara.

Ministan ya jaddada bukatar a guji yawan taruwar jama'a kana a dinga amfani da takunkumin rufe fuska ko kuma samar da wani murfi da zai yi shamaki ga baki da hanci domin rage barazanar kamuwa da cutar.

Ya zuwa daren ranar Talata, an samu sabbin mutane 117 da suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya, kuma wannan shi ne sabbin adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar da aka taba samu a kasar a rana guda, tun bayan samun rahoton farko na wanda ya kamu da cutar a Najeriya a ranar 27 ga watan Fabrairu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China