![]() |
|
2020-04-22 14:03:13 cri |
Hakika lardin Shaanxi da shugaba Xi ke rangadi a wannan karo, shi ne wurin da ya fara kiran wani taron tattauna batun rage talauci mai muhimmanci shekaru 5 da suka wuce. Don haka batun taimakawa matalauta dake wurin ya dade yana jan hankalin shugaban na kasar Sin.
A ranar Litinin da ta gabata, shugaba Xi ya shiga kauyen Jinmi na gundumar Zha'shui, inda ya fara rangadi kan aikin kawar da talauci ta hanyar raya masana'antu a can. A can baya, wannan kauye na Jinmi ya yi suna sakamakon yadda ya yi fama da talauci mai tsanani, inda mutanen kauyen 553 matalauta ne. Sa'an nan don neman samarwa wadannan mutane karin kudin shiga, jami'an kauyen sun janyo wani kamfani don ya zuba jari a can, inda aka kafa cibiyar tattara bayanai masu alaka da laimar kwadi, da rumfar shuke-suke mai kunshe da fasahohin zamani, da wurin sarrafa laimar kwadi. Ta wannan hanya na raya masana'antun sarrafa laimar kwadi, sannu a hankali an samu rage talauci a cikin kauyen, inda har aka samu kawar da talauci baki daya zuwa shekarar 2017.
Yanzu haka, ko da yake kauyen Jinmi ya kasance a wani wuri mai tsaunuka, lamarin da zai sa a dau lokaci kan a tafi wani wuri na daban, amma mutanen kauyen ba su gamu da wahala a fannin tallace-tallacen kayayyakinsu ba, domin suna iya sayar da kayansu ta kafar yanar gizo ta Intanet. Yayin da yake rangadi a can, shugaba Xi Jinping ya yi hira da wasu mutanen da suke shirin sayar da kaya ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani.
A hirarsu, mutanen sun gaya ma shugaba Xi cewa su ma'aikata ne masu kula da aikin tallace-tallacen kaya, inda suke taimakawa mutanen kauyen sayar da laimar kwadi. Sa'an nan yanzu a duk wani kauyen dake yankinsu, ana samun masu sayar da kaya ta kafar Intanet. A nasa bangare, shugaba Xi Jinping ya yaba wa wadannan mutane, inda ya ce aikin tallar kaya ta shafin yanar gizo ta Intanet yana da muhimmanci sosai ga aikin sayar da kayayyakin amfanin gona, sa'an nan ya karfafa wa wadannan masu kula da aikin tallace-tallacen kayayyaki gwiwarsu, don su kara taka rawar gani a nan gaba.
Ban da haka kuma, shugaba Xi ya ziyarci wani gari da ake kira "Laoxian", inda ya duba wani wuri mai makaurata. An sanya masu fama da talauci, ko kuma mutanen da wasu bala'u daga indallahi suka ritsa da su baki daya wasu 4173 kaura zuwa wannan wuri ne, domin a samar musu da muhallin zama mai kyau, da guraben aikin yi, ta yadda za a iya samun fid da su daga kangin talauci. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China