Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya nemi a yi kokarin cimma burin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma na bana a lokacin da ake dakile annobar
2020-04-02 13:21:21        cri

A tsakanin 29 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara tashar ruwa da masana'antu da kauyuka da kuma wurin shakatawa dake biranen Ningbo da Huzhou da kuma Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, inda ya saurari ra'ayoyin gwamnatocin wuri da na masana'antu da na jama'a kan yadda za a iya cimma burin bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar Sinawa na shekarar bana a lokacin da ake kokarin dakile annobar COVID-19.

A ranar 29 ga watan Maris, shugaba Xi Jinping ya yi rangadin aiki a yankin tashar ruwa ta Chuanshan na garin Zhoushan dake birnin Ningbo. Hukumar kula da tashar ruwa ta Chuanshan ta riga ta dauki matakai masu dacewa wajen komawa bakin aiki. Kawo yanzu yawan kayayyakin da ake shige da fice a tashar ya koma adadin da ake samu a kullum. A zauren hedkwatar tashar ruwa, Xi Jinping ya yi musayar ra'ayoyi da wakilan ma'aikatu wadanda suke aiki a tashar, inda yake fatan dukkan ma'aikatu su shawo kan illolin da annobar ta haddasa musu domin kokarin samun ci gaban da ake fata. Xi Jinping yana mai cewa, "Ina fatan dukkan ma'aikatan tashar ruwa ta Zhoushan zasu iya samun nagartaccen ci gaba kamar yadda ake fata a yayin da suke kokarin dakile matsaloli iri iri."

Bayan ya tashi daga tashar ruwa ta Zhoushan, Xi Jinping ya tafi can yankin masana'antu na Daqi na birnin Ningbo, inda ake samar da ingantattun samfurorin kayayyakin hada-hadar motoci, inda ya yi rangadi a wani karamin kamfani, wato kamfanin samar da samfurin kayayyakin hada-hadar motoci. Bayan ya saurari bayani game da yadda ake komawa bakin aiki, Xi Jinping ya nuna cewa, idan masana'antu sun iya koma bakin aiki kamar yadda ya kamata, za a iya tabbatar da ganin tattalin arzikin kasar ya bunkasa kamar yadda ake fata, sannan za a iya samar da guraben aikin yi ga ma'aikata, ma'aikata ma za su iya samun kudin shiga. Sakamakon haka, za a iya tabbatar da zaman rayuwar iyali. Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, "A lokacin da ake fuskantar bala'u daga indallahi, tabbas ne ko al'ummomi daban daban, ko masana'antu ko sana'o'i daban daban zasu fuskanci illolin da aka haddasa musu. Bisa hakikanin halin da ake ciki, kwamitin kolin JKS ya daidaita matakai domin tabbatar da rage illolin da ake haddasawa masana'antu matsakaita ko kanana, kuma domin tabbatar da ganin sun koma kyakkyawan halin da suke ciki a da, har ma zasu iya samun sabon ci gaba. Yau dalilin da yasa na zo nan shine, ina son saurarar ra'ayoyinku kan yadda zamu iya daukar sabbin matakai masu dacewa domin kokarin bunkasa tattalin arzikin kasarmu."

Xi Jinping ya kara da cewa, kamfanoni masu zaman kansu, da masana'antu kanana ko matsakaita suna da muhimmanci matuka ga bunkasar sana'o'i iri iri a kasar Sin. Yana fatan masana'antu kanana ko matsakaita su yi himma da kwazo wajen shawo kan matsalolin da suke fuskanta domin kokarin cimma yaki da annobar COVID-19.

Sannan a ranar 30 ga watan Maris, shugaba Xi Jinping ya yi rangadi a kauyen Yu na garin Anji dake karkarar birnin Huzhou. A ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2005, wato a lokacin da Xi Jinping yake kan mukamin sakataren reshen lardin Zhejiang na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya taba kai ziyarar kauyen, inda ya bayyana ra'ayinsa na "kyakkyawan muhalli shine tushen raya tattalin arziki" a karon farko. A cikin shekaru 15 da suka gabata, al'ummar kauyen Yu sun tsaya kan ra'ayinsu, na samun arziki ta hanyar bunkasa sana'o'i iri iri ba tare da gurbata muhallinsu ba.

A kauyen Yu, Xi Jinping ya nanata cewa, ana kokarin zamanintar da kasar Sin don ta zama kasa ta zamani mai sigar gurguzu daga dukkan fannoni. Ba ma kawai za'a zamanintar da birane kawai ba, har ma za a zamanintar da yankunan karkara. Yana fatan manoman kauyen Yu su kare kyakkyawan muhallinsu a lokacin da suke kokarin samun ci gaba.

A ranar 31 ga watan Maris, shugaba Xi Jinping ya yi rangadi a cibiyar kula da harkokin birnin Hangzhou, hedkwatar lardin Zhejiang, inda ya duba yadda ake warware matsalolin cunkuson motoci da na yakar annobar COVID-19 da daidaita harkoki iri iri na birnin bisa bayanan yanar gizo. Shugaba Xi ya gaya wa ma'aikatan cibiyar cewa, "Yanzu ana dakile annoba, ba a samun taruwar mutane da yawa, musamman a cikin daki. Yau na tafi can lambun shakatawa na Xixi. Bisa ka'idar wurin, idan ana son zuwa, dole ne a yi odar tikitin shiga lambun. Yawan masu shan iska da suka shiga bai iya wuce jimillar mutanen da aka iya karba a cikin lambun. A ganina, yanzu ana bukatar irin wannan mataki."

Daga karshe dai a jiya Laraba, ranar 1 ga watan Afrilu da safe, shugaba Xi Jinping ya saurarin rahoton da kusoshin reshen lardin Zhejiang na JKS da gwamnatin lardin suka gabatar masa. Xi Jinping ya nuna cewa, yanzu ana kokarin shawo kan hargitsi, amma a waje daya, akwai dama da take kasancewa a gabanmu. Yana fatan a yi kokarin bunkasa masana'antu bisa bayanan yanar gizo domin kirkiro sabbin fasahohin zamani, ta yadda za a iya samun sabon ci gaba a nan gaba. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China