Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping Ya Jagoranci Yakin Da Kasar Sin Ta Ke Yi Da COVID-19
2020-03-06 22:36:51        cri

Cutar numfashi ta COVID-19 da ta barke ta kasance babban sha'anin lafiyar jama'a na gaggawa da ta yadu cikin sauri a kasar, inda ta zama annoba mafi muni da ta barke tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Haka kuma annobar, ya zuwa yanzu, ta kasance mai wahalar sha'ani ga kasar.

Annobar ta kuma zama matsala kuma wata babbar jarrabawa ga kasar.

Ya zuwa karfe 6 na maraicen ranar 20 ga watan ga Janairu, an ba da rahoton mutane 224 da suka kamu da cutar a kasar Sin, inda aka tabbatar mutane 217 da suka kamu da cutar. 198 da suka kamu da cutar a Wuhan ne.

A ranar 20 ga watan Janairu, shugaba Xi Jinping, ya ba da umarni a mayar da hankali kan daukar matakan kandagarki da hana yaduwar cutar. Ya zuwa karshen watan Janairu, annobar ta yadu cikin sauri a lardin Hubei. A ranar 25 ga watan na Janairu, kasar Sin ta kira taron manyan shugabanni game da barkewar cutar, inda aka bayyana imani kan samun nasarar yaki da cutar. Taron ya kara yin nazari game da yanayin cutar tare da bullo da sabbin shirye-shirye game da batutuwan da suka shafi jinyar marasa lafiya.

Xi ya jagoranci taruka guda shida na manyan shugabanni game da aikin kandagarki da hana yaduwar cutar cikin kwanaki 40 tsakanin ranar 25 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Maris.

A ranar 2 ga watan Fabrairu, shugaba Xi, kana shugaban kwamitin koli na rundunonin sojojin kasar, ya amince a tura ma'aikatan lafiya sojoji 1,400 zuwa asibitin Huoshenshan dake Wuhan domin kula da marasa lafiya, tun daga ranar 3 ga watan Fabrairu. Daga bisani, an sake tura karin ma'aikatan lafiya sojoji 2,600 zuwa garin na Wuhan don su taimaka.

A ranar 10 ga watan Fabrairu, Xi ya duba aikin kandagarki da hana yaduwar cutar COVID-19 a Beijing, inda ya yi nuni da cewa, ya kamata Hubei, musamman Wuhan, ya kasance inda za a ba da muhimmanci a aikin kandagarki da hana yaduwar cutar. Wuhan shi ne muhimmin wurin da za a yi kokarin cimma nasarar yaki da COVID-19. Idan Wuhan ya yi nasara, to Hubei ya yi nasara. Idan Hubei ya yi nasara, to baki dayan kasar Sin ce ta yi nasara.

A ranar 3 ga watan Fabrairu, Xi ya jaddada cewa, kasar tana bukatar hadadden tsari na hana yaduwar cutar. A lokacin da Hubei yake bukatar kayayyakin kiwon lafiya, ya kamata kamfanoni daga sassan kasar su samar tare da raba su.

A ranar 2 ga watan Maris, Xi ya duba yadda aka gudanar da ayyukan binciken kimiyya game da COVID-19 a Beijing, inda ta ziyarci cibiyar kimiyyar likitanci ta Soja da jami'ar Tsinghua, don sanin irin ci gaban da aka samu a fannin binciken alluran rigakafi, binciken yanayin cutar, da fasahar gano cutar. Ya ce, babban makami na yaki da cutar, shi ne kimiya da fasaha. A cibiyar kimiyar likitanci ta soja, da samun wannan umarni na shugaba Xi, nan da nan jagoran tawagar masanan, Chen Wei, suka fara gudanar da binciken kimiyya ba dare ba rana. Tawagar ta samu gagarumin ci gaba a bincken da take gudanarwa game da alluran riga kafi.

Xi, ya bayyana cewa, babu tantama barkewar cutar COVID-19 za ta yi matukar tasiri kan tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Ko da ya ke, a halin yanzu, abu mai muhimmanci shi ne, a kalli ci gaban kasar Sin daga dukkan fannoni, da ma dogon lokaci tare da kara imani da muke da shi.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China