Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya yi rangadi a wani kauyen dake lardin Zhejiang
2020-03-31 12:16:32        cri

A jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ci gaba da rangadinsa a lardin Zhejiang dake gabashin Sin, inda ya shiga kauyen Yu dake gundumar Anji.

Wannan ba shi ne karo na farko da shugaba Xi ya yi rangadi a kauyen Yu ba. Ko a shekarar 2005, lokacin da yake aiki a matsayin babban sakataren reshen kwamitin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake lardin Zhejiang, ya taba shiga kauyen, inda ya yaba kan yadda aka daina wasu harkoki na hakar ma'adinai, da samar da siminti a wurin, tare da bayyana ra'ayinsa na "kyakkyawan muhalli shi ne tushen raya tattalin arziki" a karon farko.

"Kar mu ci gaba da bin wasu tsoffin hanyoyin raya tattalin arziki. Kun ce za ku daina hakar ma'adinai, wannan ya nuna hikimarku. Domin kyan muhalli shi ne tushen raya tattalin arziki. A baya mun ce za mu so muhalli mai kyau, gami da raya tattalin arziki. Amma a hakika kare muhalli da raya tattalin arziki aiki guda ne."

Bayan an daina fitar da ma'adinai daga kauyen Yu, sai aka mai da hankali ga fannin raya aikin yawon shakatawa a can, inda aka bude wuraren nishadantarwa, da dakunan masaukin baki, da gudanar da wasan gadon fito. Bayan an kwashe shekaru fiye da 10 ana kokarin raya harkoki a kauyen Yu, an samu damar canza wannan kauye, wanda a baya ke fama da matsalar gurbacewar muhalli, zuwa wani shahararren wurin da ake son zuwa yawon shakatawa.

Bayan da shugaba Xi ya kammala ziyararsa a kauyen Yu, ya ci gaba da rangadinsa a wata cibiya mai kula da aikin daidaita rigingimun da a kan samu tsakanin jama'a dake gundumar Anji.

Kafin haka, wato a ranar Lahadin da ta gabata, shugaba Xi Jinping ya taba yin rangadi a tashar jiragen ruwa ta Chuanshan, da wani yankin masana'antu na samar da na'urorin da ake yin amfani da su wajen kera motoci, inda ya yi bincike kan yadda ake farfado da ayyuka a wadannan wurare, bayan da aka samu shawo kan yanayin bazuwar cutar COVID-19 a kasar Sin. Sa'an nan a cikin yankin masana'antun, ya yi mu'ammala da wasu ma'aikata, inda ya bayyana cewa:

"Yanzu muna kokarin dakile yaduwar annoba, gami da neman farfado da ayyukan samar da kayayyaki. Ya kamata mu gudanar da aikin samar da kayayyaki yadda ake bukata, gami da tabbatar da lafiyar kowa."

A cikin cibiyar kula da ayyuka da samar da hidimomi ta wannan yankin masana'antu, shugaba Xi Jinping ya tattauna da shugabannin yankin, da wasu masu kananan kamfanoni, gami da wasu ma'aikata da suka koma bakin aikinsu daga sauran yankunan kasar, inda shugaban ya ce:

"Bayan barkewar annoba, wadda ta kansace wata babbar matsala, da bala'i daga Indallahi, dukkan gugun mutane, da kamfanoni, da sana'o'i daban daban, na shan wahala. Sai dai yayin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke kokarin neman dabara don tinkarar annobar, ya lura sosai kan kanana da matsakaitan kamfanoni."

Shugaban ya ce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gabatar da wasu manufofi don tallafawa wadannan kamfanoni masu zaman kansu. Sa'an nan za ta ci gaba da daidiata manufofi bisa canzawar yanayin da ake ciki, don biyan bukatun kamfanonin, da kare su daga illolin da annobar COVID-19 ta haifar. Ta yadda za a tabbatar da ganin farfadowar kamfanonin cikin sauri, gami da ci gaban harkokinsu a fannoni daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China