Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane irinsu Pompeo na kara damuwa a yayin da suke kokarin shafa wa wasu kashin kaza
2020-04-18 17:01:19        cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya bada amsar cewa za a gudanar da cikakken bincike, a lokacin da aka masa tambaya a ranar 15 ga wata, kan ko cutar COVID-19 ta samo asali daga cibiyar gwajin cututtuka ta birnin Wuhan.

Sai dai daga bisani, a yayin da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ke zantawa da manema labarai, ya furta cewa, wai cutar ta samo asali daga birnin Wuhan.

 

 

Furucin Mr.Pompeo ya zo ne kwana daya tak, bayan ya tattauna da wani babban jami'in kasar Sin mai kula da harkokin waje, inda a yayin tattaunawar, ya ce annobar kalubale ne na bai daya da kasa da kasa ke fuskanta, kuma Amurka na son hada kai da kasar Sin, don tabbatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma, na karfafa hadin gwiwar kasashen biyu ta fannin shawo kan cutar. Sai dai yadda Mr.Pompeo ya sake mayar da hankalinsa kan zargin kasar Sin, ya sake shaidawa duniya yadda manyan jami'an kasar kan yi amai su lashe.

Tabbatar da asalin cutar aiki ne na masu nazarin kimiyya, a maimakon 'yan siyasa su yanke shawara yadda suka ga dama. Sau da dama, hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, babu abin da zai iya tabbatar da cewa, cutar ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje. Sai dai 'yan siyasar Amurka ba su lura da hakan ba, inda suke ta mayar da hankalinsu kan dorawa kasar Sin laifi.

A yanzu haka, wasu 'yan siyasar Amurka suna kokarin neman fid da kansu daga mawuyacin halin da suke ciki. Kamar yadda wakilin kafar CNN Jim Acosta ya bayyana a wani shirin da aka watsa a ranar 14 ga wata cewa, shugaban Amurka na kokarin gano hanyoyin kawar da hankalin al'umma, kuma idan aka yi waiwaye, WHO da kafofin watsa labarai da 'yan jam'iyyar Democrat da gwamnonin jihohi daban daban duk suna cikin wadanda shugaban ya dora wa laifin yaduwar cutar, sai dai ya zargi kowa ban da shi kansa.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China