Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa kasar Amurka ta sauya halinta daga tabbaci zuwa rudani?
2020-04-16 21:43:35        cri

Ya zuwa yanzu, jihohi 40 da birnin Washington D.C da ma yankunanta dake ketare guda hudu dukkansu suna fuskantar babbar masifa sakamakon yaduwar cutar COVID-19, wannan yanayi ba a taba ganin irinsa a tarihin kasar Amurka ba.

Tun daga ranar 3 ga watan Janairu, kasar Sin ta soma sanar da yanayin annobar ga hukumar WHO da ma kasashe daban daban, ciki har da Amurka.

Rahotannin da kafofin watsa labarun kasar Amurka suka fitar na nuna cewa, shugaban hukumar lafiya da jin dadin jama'a ta kasar HHS Alex Azar ya ba da rahoto da yin gargadi ga shugaban kasar Donald Trump a ranar 18 ga watan Janairu da karshen watan Janairu kan annobar cutar. Ban da wannan kuma, jami'an gwamnatin kasar da dama da mashawarta da kuma kwararru a fannin bayanan sirri su ma sun tabbatar da wannan barazana, kana sun bayyana cewa, dole ne a dauki matakan da suka wajaba. Amma, har zuwa ranar 21 ga watan Janairu, wato lokacin da aka gano mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar, ba a soma aikin dalike cutar ba.

A ranar 29 ga watan Janairu, fadar White House ta kafa kwamitin dalike cutar COVID-19, amma sun mayar da hankali ne kan batutuwa kamar kwashe 'yan kasar dake ketare.

A ranar 29 ga wata, jihar Washington ta ba da rahoton mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar a kasar, sannan aka ayyana dokar ta baci. Tun wannan lokaci, jihohi da dama su ma sun ayyana irin wannan dokar ta baci.

A ranar 13 ga watan Maris, Donald Trump ya sanar da cewa, Amurka ta ayyana dokar ta baci, sakamakon annobar COVID-19, kuma da soma aikin dalike cutar a dukkan fannoni. Yanzu haka, kwanaki 70 ke nan da suka gabata, tun lokacin da aka gargadi gwamnatin kasar kan wannan annoba.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China